You are here: HomeAfricaBBC2022 10 12Article 1641416

BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

Yaya magungunan tarin da ake zargi da kisan yara suka je Gambia?

Hoton alama Hoton alama

Ana gudanar da bincike kan dokokin yin magunguna da kuma kasuwancinsu a duniya, bayan mutuwar yara kusan 70 a kasar Gambia da aka alakanta da amfani da wasu magungunan tari na ruwa wadanda aka yi a Indiya ta tayar da hankalin jama'a. Mene ne ya haifar da matsala a Gambia? A makon da ya gabata hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta fitar da wata sanarwa inda ta yi gargadin amfani da wasu magungunan tari na ruwa guda hudu, inda ta ce za su iya kasancewa sanadin mummunar cutar koda da rahotanni ke cewa ana samun yara a kasar Gambia da ita. Hukumar lafiyar ta ce binciken da aka yi ya nuna cewa magungunan suna dauke da wasu sinadarai ( diethylene glycol da ethylene glycol ) wadanda yawansu ya wuce ka'ida matuka wanda hakan illa ne ga koda. Hukumomin Indiya da kamfanin da ya yi magungunan (Maiden Pharmaceuticals), sun ce Gambia kadai aka kai magungunan. Abin da muka sani game da kamfanin magungunan Kamfanin na Maiden Pharmaceuticals ya ce yana bin dukkanin dokokin hada magunguna na duniya. To amma wasu daga cikin magungunansa ba su cika dokoki da ka'idojin da ya kamata a ce sun cika ba a matakin jiha ko ma a matakin kasar Indiya. Bayanan hukuma sun suna cewa: 1- Jihar Bihar ta soke sunan kamfabin a 2011, saboda samunsa da laifin sayar da maganin tari na ruwa da bai cika ka'idoji ba. 2- A 2018 hukumra kula da ingancin magunguna ta Indiya ta gurfanar da shi a gaban kotun saboda rashin cika ka'ida. 3- Kamfanin ya fadi jarrabawar gwaji da aka yi wa magungunansa a jihar Jammu da Kashmir a 2020 4- Sau hudu yana faduwa jarrabawar da aka yi masa a jihar Kerala a 2022.  Haka kuma kamfanin yana daga cikin kusan kamfanoni 40 na Indiya wadanda gwamnatin Vietnam ta soke sunansu saboda shigar da magungunan da ba su da inganci sosai.  Kamfanin wanda ke da mazauni a jihar Haryanzu ya ce ya kadu matuka da mace-macen da aka samu a Gambia.  Kuma ya ce shi kam yana bin dukkanin ka’idojin aiki da hukumomin lafiya suka gindaya, na kasar ta Indiya da ma jihar da yake ta Haryana. Martanin kamfanin Ko da BBC ta nemi jin ta bakin hukumomin kamfanin a game da zargin mace-macen yaran a Gambia, sun ce ba za su kara magana ba a kai saboda hukumomi na gudanar da bincike a kan magungunan. Ministan lafiya na jihar Haryana Anil Vij ya gaya wa BBC cewa an dauki magunguna ana gwaji a kansu kuma idan har aka samu wani abu ba daidai ba za a dauki mataki a kai. Yaya ingancin aikin hukumomin Indiya yake?Indiya ce ke samar da kashi daya bisa uku na yawan magungunan duniya. Ita ce babbar mai samar da magunguna ga kasashen Afirka da Latin Amurka da sauran sassan Asiya. Ana bukatar kamfanoninta su bi tare da kiyayewa da tsauraran matakai da ka’idoji na  yin magunguna.  To amma kamfanonin Indiya sukan fuskanci matakai har da ma dakatarwa daga hukumomin wasu kasashe kamar na Amurka saboda saba ka’idoji a wasu kamfanonin magunguna na kasar. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa hukumomin da ke sanya ido a kan kamfanonin na Indiya suna fama da karancin kudi da kuma gaza tabbatar da bin ka’idojin da suka kamata wurin ayyukan kamfanonin.  Wani mai rajin kare lafiyar jama’a, Dinesh Thakur yan una yadda babu hukunci mai tsanani da ake yi wa wadanda suka saba ka’ida a kasar ta Indiya. Hukuncin da ake yin a saba ka’ida shi ne tarar dala 242 da kuma watakila idan har ta kama daurin da ya kai na shekara biyu a gidan yari. Ya ce ‘’sai dai idan har an tabbatar da wani magani maras inganci yana da alaka kai tsaye da mutuwa, idan ba haka ba wannan shi ne hukuncin da ake yi,’’ Haka kuma Indiya ba ta cikin tsarin Hukumar Lafiya ta Duniya na hukumo,min da ke sanya ido wajen bin ka’idojin yin magunguna, kodayake tana cikin masu lura da yadda ake alluran riga-kafi. ‘’Wannan zai iya sanya wa a samu rashin bin ka‘idoji sau da kafa yadda ya kamata a ayyukan kamfanonin yin magunguna,’’ in ji Leena Menghaney, ta kungiyar likitoci ta duniya (Médecins Sans Frontières) a kudancin Asiya.  Ya kamata a ce Gambia ta yi gwaji tun da farko? Ma’aikatar lafiya ta kasar Indiya ta fara gudanar da bincike a kan mace-macen da suka auku a Gambia, amma kuma ta ce a ka’ida kamata ya yi a ce duk wata kasa da ta sayi magani daga wani kamfani na Indiya ta tabbatar ta yi gwajinsa, ta tabbatar ta gamsu da ingancinsa. To amma shugaban hukumar kula da ingancin magunguna ta Gambiya Markieu Janneh Kaira ya ce hukumar tana bayar da fifiko ne a gwajin magunguna zazzabin cizon sauro da na rage radadi da makamantansu amma ba ruwan magani na tari ba. BBC ta tuntubi hukumar amma kuma hukumomin ba su yi magana ba Shugaban kasar ta Gambiya, Adama Barrow, ya ce za su tabbatar sun gudanar da bincike kan lamarin. Sannan ya kafa wani dakin bincike na kasa da zai rika tabbatar da inganci da lafiyar magunguna. Ya kara da cewa ‘’Gambia za ta kafa ka’idoji domin kawar da magunguna marassa inganci.’’ Kungiyar likitoci ta duniya MSF, ta ce tana son kungiyoyin da ke da wadatattun kayan gwaji da su rika taimaka wa kasashe talakawa irin su Gambiya.  Wata jami’ar hukumar Ms Menghaney ta ce, "wannan ba wai aiki ne da ya rataya a kan kasashe masu sayen maganin ba kawai."  A Najeriya hukumar da ke kula da ingancin magani da abincici, NAFDAC a yanzu ta umarci da a tabbatar jami’an da suka cancanta sun tantance ingancin duk wani magani da za a shigar kasar daga Indiya.