You are here: HomeAfricaBBC2022 10 12Article 1641419

BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

Peter Obi ya kare matakinsa na jinkirta fitar da manufofinsa

Peter Obi Peter Obi

Dan takarar shugabancin Najeriya karkashin jam'iyyar Labour Peter Obi, ya ce yana jiran manyan kungiyoyin kwadago na kasar kafin ya fitar da manufofinsa. Ana dai ta sukar dan takarar saboda rashin fitar da manunfofinsa da shirin da ya yi wa kasar idan an zabe shi, makonni biyu bayan fara yakin neman zabe a hukumance, abin da ya sa masu sukar ke cewa dan takarar bai shirya zama shugaban kasar ba. To sai dai a wata tattaunawa da BBC mista Obi ya ce, ba wai Najeriya ta rasa dabaru ko rubutattun tsare-tsare ba ne. Sai dai tana fuskantar "tsari mara nagarta da kuma rashin karfin gwiwwa a bangaren masu mulki domin aiwatar da tsare-tsare masu kyau. Mista Obi, wanda ya taba yin gwamna har karo biyu a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya - yankin da ake samun karuwar masu kiraye-kirayen ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafra - ya bayyan yadda zai jagoranci kasar idan aka zabe shi. Ya kara da cewa ''babban abin da Najeriya ke bukata shi ne magance matsalar tsaro, wannan matsala ce da ta yi wa kasar kaka-gida, wacce ke bukatar a maida hankali wajen kawo karshenta''. ''Idan ka kawar da matsalar tsaro yau, to ka magance matsalar hauhawar farashin kayayyaki, saboda manoma za su koma gonakinsu domin noma abincin da kasa ke bukata, kuma yin hakan zai rage hauhawar farashin kayayyaki'', in ji mista Obi. Yayin da ya rage 'yan watanni a fita filin zaben da za a fafata tsakanin manya kuma fitattun 'yan takara, rashin fitar da manunfofin dan takarar ka iya kawo masa cikas ga yunkurinsa na samun nasarar darewa shugabancin kasar da ta fi kowacce kasa yawan al'uma nahiyar Afirka.