You are here: HomeAfricaBBC2022 10 12Article 1641413

BBC Hausa of Wednesday, 12 October 2022

Source: BBC

Yadda jiragen yakin Najeriya suka kashe rikakken mai garkuwa da mutane Ali Dogo da yaransa

Jirgen yaki na Najeriya Jirgen yaki na Najeriya

Rundunar sojin saman Najeriya ta bayyana yadda jiragen yakinta suka yi luguden wuta kan rikakken mai garkuwa da mutanen nan Ali Dogo da wasu yaransa a Jihar Kaduna da ke arewacin kasar. Mai magana da yawun rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya tabbatar wa BBC Hausa faruwar lamarin. Air Commodore Gabkwet ya ce bayanan sirrin da suka samu sun nuna cewa Ali Dogo da yaransa sun taru a gidan wani fitaccen mutum da ke karamar hukumar Giwa a Jihar Kaduna domin kitsa yadda za su kai hare-haren ta'addanci da garkuwa da mutane a karshen makon jiya. A cewarsa: "Da ma mun dade muna nemansa, don haka da jin wannan labarin sai muka tura jiragen yakinmu gidan Alhaji Gwarzo a kauyen Yadi na karamar hukumar Giwa inda suka yi luguden wuta kan dukkan 'yan ta'addan da ke wurin. Allah ya ba mu sa'a mun kashe Ali Dogo da mayakansa talatin." Ya kara da cewa dan fashin dajin da mayakansa sun gudu daga Jihar Neja ne zuwa Kaduna sakamakon hare-haren da sojojin sama suke yawan kai musu. Mai magana da yawun sojin saman na Najeriya ya ce Ali Dogo ya shahara wurin yin garkuwa da mutane, yana mai cewa "shi ne dan fashin dajin da ke kashe mutanen da ya kama idan aka hana shi kudin fansa."