You are here: HomeAfricaBBC2021 03 17Article 1206817

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: bbc.com

NBS: Jihohin da kayan abinci suka fi tsada a Najeriya

Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya bambanta tsakanin jihohin ƙasar kamar yadda rahoton hukumar ƙididdiga ta kasar ya nuna.

Rahoton na hukumar ƙididdigar ta Najeriya wato NBS ya ce an samu hauhauwar farashin da ya kai kashi 17.33 cikin ɗari a watan Fabrairun da ya wuce.

Alƙaluman sun nuna cewa tashin farashin ya ƙaru ne da kashi 1.54 a Fabrairun 2021 idan aka kwatanta da kashi 1.49 a watan Janairu. Kuma farashin kayan abinci ya tashi da kashi 21.79 a Fabrairun da ya gabata idan aka kwatanta da kashi 20.57 a watan Janairu.

Hukumar ta ce wannan ne karon farko da aka samu irin wannan tashin farashi a cikin shekaru hudu da suka wuce.

Alƙaluman hukumar sun nuna farshin kayan abinci ya yi tashin gwauron-zabo a makwanni biyun da suka wuce lokacin da kungiyar fataken dabbobi da kayan abinci da ƴaƴanta suka yi yaji inda har ta kai ga sun datse hanyar kai kayayyaki daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci.

Rahoton ya nuna cewa tashin farashin kayan abinci ya shafi kayan abinci irin su burodi da nama da kifi da dankali da kuma farashin kayan miya da na kayan marmari ko kayan lambu.

Ina kayan abinci suka fi tsada?

Alƙaluman hukumar sun ce a ma'aunin shekara shekara, jihar Kogi aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci da kashi 30.47.

Sai jihar Ebonyi da kashi 25.73 da kuma jihar Sokoto da kashi 25.68.

Rahoton ya ce jihohin da farashin kayan abincin bai tashi ba sosai sun haɗa da Gombe da ke da kashi 19.32 da Bauchi da ke da kashi 18.74 da kuma Akwa Ibom da ke da kashi 18.70.

Haka ma a maunin wata-wata, rahoton ya ce jihar Kogi ce aka fi samun hauhawar farashin kayan abinci tsakanin Janairu zuwa Fabrairu da kashi 3.34.

Sai jihar Ondo kashi 3.33 da Ebonyi kashi 3.26.

Jihohin da farashin kayan abincin bai tashi ba a wata-wata sun haɗa da Benue da Neja da ke da kashi 0.90 sai Kano mai kashi 0.70 da Oyo mai kashi 0.09

Me ya janyo hauhawar farashin?

Masana na ganin dalilai da yawa ne suka janyo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya kasar da tattalin arzikinta ke dogaro da arzikin fetir.

Shuaibu Idris Mikati masanin tattalin arziki a Najeriya ya ce an samu hauhawar farashi saboda yawancin abubuwan da ake amfani da su shigowa da su ake yi a ƙasar.

Sannan kuma dole idan canjin kuɗi ya karu kamar darajar naira ta yi ƙasa farashin kayayyaki dole ya ƙaru.

"An samu hauhawar farashi saboda yanayin canji a Najeriya," in ji shi.

Haka kuma masanin na ganin tanzomar EndSars ta kara haifar da tsadar kayayyaki da kuma yajin aikin masu dakon kaya daga yankin arewaci zuwa kudancin Najeriya.

Masanin ya bayyana cewa yajin da masu fataucin suka yi ya nuna yadda ɓangarorin Najeriya suke dogaro da juna ta fuskar tattalin arziki:

Rahoton hukumar ƙididdigar na zuwa a yayin da ake fama da wata taƙaddama kan ƙarin farashin mai a Najeriya, bayan hukumar da ke kula da farashin mai ta kasar ta fitar da wata sanarwa da ta nuna farashin litar man fetur zai hau zuwa fiye da naira dari biyu. Ko da yake daga baya ta janye sanarwar.

Ana ganin rudanin ya haddasa ƙarin farashin kayan masarufi a Najeriya inda mafi yawanci farashin fetir ke tasiri ga farashin kayayyaki a ƙasar.

Kuma masana na ganin sai gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa don magance yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa.

Join our Newsletter