You are here: HomeAfricaBBC2021 03 17Article 1206823

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Milenkovic, Haaland, Ronaldo, Goncalves

Dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo Dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo

Manchester United ta soma tattaunawa da wakilin dan wasan Fiorentina dan kasar Serbia mai shekara 23, Nikola Milenkovic. (Calciomercato - in Italian)

Fitaccen dan wasan NBA LeBron James ya zama abokin harkokin kasuwancin kamfanin Fenway Sports Group, wanda ya mallaki Liverpool - kungiyar da yake da hannun jari a cikinta tun 2011. (Boston Globe, via Liverpool Echo)

Liverpool na duba yiwuwar neman daukar dan wasan tsakiyar Norway dan shekara 23 Sander Berge daga Sheffield United a bazara. (Eurosport)

Mai yiwuwa dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai fi son komawa Manchester United maimakon Real Madrid idan ya bar Juventus a bazara. (Tuttosport - in Italian)

Mutumin da ya mallaki Chelsea Roman Abramovich yana so ya dauki gabaran dauko dan wasan Norway Erling Braut Haaland, mai shekara 20, daga Borussia Dortmund a bazara. (Star)

Dan wasan Sporting Lisbon dan kasar Portugal da ke buga gasar Under-21 Pedro Goncalves, mai shekara 22, ya zama dan wasan da Manchester United take son daukowa a rahusa idan ta gaza dauko dan wasan Ingila mai shekara 20 Jadon Sancho daga Borussia Dortmund. (Telegraph - subscription required)

Yunkurin Manchester United na dauko dan wasan Sevilla Jules Kounde, mai shekara 22, ya samu tagomashi a yayin da kungiyar ta Sifaniya ta rage farashin da ta sanya kan dan wasan na Faransa zuwa kusan £50m. (Sun)

Dan wasan Arsenal Matteo Guendouzi, mai shekara 21, ya ce zai yi aiki tukuru domin ya burge kocin kungiyar Mikel Arteta idan ya kammala zaman aron da yake yi a Hertha Berlin a karshen kakar wasan bana. (France Football - in French)

Tottenham na son sayar da dan wasan Colombia mai shekara 24 Davinson Sanchez a bazara kuma tuni suka soma neman dan wasan da zai maye gurbinsa. (Football Insider)

Ana alakanta Chelsea da yunkurin daukar dan wasan Palmeiras mai shekara 20 dan kasar Brazil Gabriel Menino, wanda Atletico Madrid take son dauka. (UOL, via Sport Witness)