You are here: HomeAfricaBBC2021 03 17Article 1206814

BBC Hausa of Wednesday, 17 March 2021

Source: BBC

Wasika daga Afirka: Abin da shugaban Faransa Macron bai fahimta ba game da mulkin mallaka

Shugaban Faransa Emmanuel Macron Shugaban Faransa Emmanuel Macron

A cikin jerin wasiƙun da muke samu daga 'yan jaridar Afirka, dan jaridar Canada dan asalin Algeria Maher Mezahi ya yi waiwaye kan yunkurin baya bayan nan da Faransa ta yi na dinke barakar da ke tsakaninta da tsohuwar kasar da ta yi wa mulkin mallaka - Algeria, musamman game da yakin da aka fafata na neman 'yanci.

Shin shugaban Faransa Emmanuel Macron ya fahimci tasirin mulkin mallaka?

Na yi wannan tambaya ce sakamakon abin da ya faru a baya bayan nan - amincewar da dakarun sojin Faransa suka yi na azabtarwa da kuma kashe dan kishin kasar nan na Algeria Ali Boumendjel - bayan kwashe shekara 60 suna musanta yin hakan.

Sun dauki wannan mataki ne a matsayin jerin matakai da ake son dauka na sasanta dangataka tsakanin Faransa da Algeria bayan an kwashe shekara fiye da dari ana mulkin mallaka wanda ya zo karshe a 1962, bayan an kwashe shekara takwas ana yaki.

Martanin da 'yan kasar Algeria suka yi game da kalaman Mr Macron ba yabo ba fallasa.

Watakila sun yi hakan ne saboda sako mai harshen damon da ya aike game da abubuwan da suk faru a baya.

Karon farko da 'yan kasar Algeria suka ji daga Mr Macron shi ne lokacin da ya ziyarci kasar a watan Fabrairun 2017 yayin da yake takarar shugabancin kasarsa.

A wata hira da ya yi, ya yi tsokaci fiye da yadda kowanne shugaban Faransa ke yi inda ya bayyana mulkin mallaka a matsayin "laifin da aka yi kan dan adam".

Tsokacin da ya yi na ba kasafai ba ya bai wa galibin 'yan kasar Algeria mamaki. Kuma sun yi tasiri kan siyasar 'yar takarar jam'iyyar da ke da tsaurin ra'ayi, Marine Le Pen

A karon farko a rayuwata, na ji cewa akwai yiwuwar samun shugaban Faransa wanda zai fito fili ya fayyace dangatakar tarihi tsakanin Faransa da Algeria, abin da zai bayar da damar kulla sabuwar dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Amma tun da ya zama shugaban kasa, Mr Macron ya yi ta yin baki biyu game da harkokin Algeria.

Fitattun ranakun tarihitsakanin Faransa da Algeria

1830: Faransa ta mamaye Algiers

1848: Bayan hatsaniyar da shugaban 'yan tawaye Abd-el-Kader ya jagoranta, Paris ta ayyana Algeria a matsayin wani bangare na Faransa

1940: Faransa ta fada hannun Jamus a Yakin Duniya na Biyu

1942: Sojojin Ingila da Amurka sun isa Algeria

1945: Sojojin Ingila da Amurka sun yi nasara kan Jamus. An kashe dubbana mutane a wani bore na neman 'yanci a Sétif

1954-62: Yakin Algeria

1962: Algeria ta samu 'yanci kai

Amincewar da dakarun Faransa suka yi na kisan Boumendjel bai jawo martni mai yawa ba a nan saboda, kamar yadda masana tarihi da masu ilimi mai zurfi suka rubuta, ba shi da wani tasiri a bayyana wasu daga cikin mutanen da lamarin ya shafa sannan a bar wasu da dama.

Wani masani ya bayyana cewa wannan lamarin ne da ya shafi harkokin "Faransa" issue, abin da ke nufin cewa ba domin 'yan kasar Algeria Mr Macron ya yi kalaman ba.

Kazalika, ofishinsa ya ce ba zai fitar da sanarwar neman afuwa ba.

Kasa da shekara daya bayan ya ziyarci Algeria a matsayin dan takara, Mr Macron ya koma kasar a matsayin shugaban kasa.

Ya ziyarci birnin Algiers tare da wakilan 'yan siyasa da masana tarihi da kuma tarin jami'an tsaro.

Yagaisa da mutane sannan ya dauki hotunan dauki-kanka wato selfie tare da mutanen da ke kallonsa kafin wani matashi ya bayyana cewa: "Dole ne Faransa ta yarda da abubuwan tarihin na mulkn mallaka da ta yi a Algeria".

Bayan sun tattauna da matashin, Mr Macron ya mayar da martanin cewa: "Amma ba ka san mulkin mallaka ba!

"Me ya sa kake damuna da wannan magana? Ya kamata matasa irinka su mayar da hankali kan makamarsu."

Bayan na ji wadannan kalamai nasa, na yi saurin fahimtar cewa duk da tsare-tsarensa na ci gaba a kan Algeria, Mr Macron bai fahimci abin da yake son cimma ba.

Ya maimaita irin wadannan kamalai a kasashen Yammacin Afirka da dama.

"Daya bisa uku na 'yan kasarku ba su taba ganin mulkin mallaka ba," a cewarsa lokacin da ya je Ivory Coast.

A Burkina Faso ya shaida wa dalibai cewa da su da shi ba su san mulkin mallaka ba.

Babu wanda zai yi irin wannan kalami sai wanda ba shi da masaniya kan rayuwa bayan mulki mallaka.

Dukkan 'yan kasar Algeria sun fuskanci matasalar da mulkin mallakar Faransa ya haifar.

An sanya wa makarantunmu da titunanmu da filayen wasanmu sunayen masu fafutukar juyin juya hali.

Gine-ginemu da abincinmu da yarukanmu sun fuskanci tasiri daga mulkin mallakar da turawa suka kwashe shekara 132 suna yi mana.

Dangina ba su taka rawa game da fafutukar juyin juya hali ba, amma kakana na cikin dubbana 'yan kasar Algeria da suka fuskanci matsala a Ligne Morice - wata rijyar hakar ma'adinan kasa da Faransa ta gina a kan iyakar Algeria daga yankin gabas.

A matsayinsa na yaro da ya girma a Tebessa, ya rika tsallake tarkon da aka rika danawa wanda ya rika yin bindiga a kan idanunsa.

Nakan tuna da shi duk lokacin da na kira mahaifina, wanda aka sanya wa sunansa.

Gwamnatin Faransa ba ta fitar da tasawirar rijiyoyin hakar ma'adinan da ta haka a fadin iyakar Algeria daga gabashin kasar ba sai a shekarar 2007.

Sojojin Faransa sun kwashe tsawon shekarun 1960 suna yin gwajin bama-bamai 17 a yankin Sahara na Algeria.

Daruruwan dubban mutanen da ke zaune a yankunan da lamarin ya faru sun yi fama da matsalolin rashin lafiya irin su ciwon daji sakamakon wannan aiki.

Har yanzu Faransa ba ta fitar da tasawirar wuraren da ta yi gwajin bama-baman nukiliya a kasar ba.

Aakasarinmu matasan Algeria ba ma tsammanin Faransa za ta nem afuwa.

Abin da kawai muke son gwamnatin Mr Macro ta yi shi ne ta fito fili ta bayyana gaskiya game da laifukan da Faransa ta tafka a Algeria da ma nahiyar Afirka.