You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776764

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Liverpool ta nada Schmadtke daraktan wasanninta

Liverpool ta sanar da daukar Jorg Schmadtke a matakin sabon daraktan wasanninta Liverpool ta sanar da daukar Jorg Schmadtke a matakin sabon daraktan wasanninta

Liverpool ta sanar da daukar Jorg Schmadtke a matakin sabon daraktan wasanninta.

Schmadtke, mai shekara 59, ya maye gurbin Julian Ward, wanda ya yi shekara 11 yana aiki da kungiyar ta Anfield.

Ya yi aikin daraktan wasanni a Worlfsburg, da ke buga Bundesliga, inda ya bar aikin a watan Fabrairu.

Schmadtke, wanda mai tsaron raga ne a lokacin da ya taka leda, ya yi kaka hudu da rabi a Wolfsburg a matsayin daraktan wasanninta.

A lokacin ne kungiyar ta samu gurbin shiga Champions League, bayan da ta yi ta hudu a teburin Bundesliga a 2020-21.

Liverpool, wadda ta ci karo da kalubale a kakar nan ta kammala Premier League a mataki na biyar, ba za ta buga Champions League a badi ba.

Kungiyar ta Anfield za ta kara a Europa League a kaka mai zuwa, karon farko da ta fice cikin 'yan hudun farko a teburin Premier tun bayan 2016-17.

A wasannin Champions League a bana, Real Madrid ce ta fitar da Liverpool, yayin da aka yi waje da ita a zagaye na hudu a FA Cup da kuma EFL Cup.

Kungiyar Anfield za ta sayo 'yan wasa da zarar an bude kasuwar cinikin 'yan kwallo ta bana, bayan da 'yan wasanta hudu za su barta a karshen kakar nan.

'Yan wwasan sun hada da James Milner da Naby Keita da Alex Oxlade-Chamberlain da kuma Roberto Firmino.