You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776767

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Wadanda aka bai wa jan kati da yalo a Premier League ta bana

Hoton alama Hoton alama

Ranar Lahadi aka kammala gasar Premier League ta kakar 2022/23, wanda Manchester City ta lashe.

Tuni aka samu wadanda suka bar premier league a kakar da aka karkare, za su koma buga Championship a badi.

Sai dai kuma an bai wa 'yan wasa da yawa jan kati da kuma mai ruwan dorawa a wasannin bana.

Hakan ne ya sa muka hada muku wasu jerin 'yan kwallon Premier League da suka karbi katin gargadi da yawa da wadanda aka bai wa jan kati a kakar nan.

Jerin goman farko a 'yan wasan da suka karbi kati mai ruwan dorawa:

Kungiya Yawan katin Yawan laifi Kungiya


  1. Joao Palhinha 14 48 Fulham
  2. Joelinton 12 65 Newcastle
  3. Rúben Neves 12 38 Wolves
  4. Nelson Semedo 11 47 Wolves
  5. Fabinho 11 53 Liverpool
  6. Adam Smith 11 29 Bournemouth
  7. James Maddison 10 31 Leicester
  8. Moisés Caicedo 10 65 Brighton
  9. Conor Gallagher 9 23 Chelsea
  10. Boubakary Soumaré 9 33 Leicester

Jerin goman farko da aka bai wa jan kati a gasar Premier League:


Kungiya Yawan kati Yawan laifi Kungiya

  • Casemiro 2 48 Man Utd
  • Nathaniel Chalobah 1 2 Fulham
  • Lucas Moura 1 3 Tottenham
  • James Tomkins 1 3 Crystal Palace
  • Mason Holgate 1 9 Everton
  • Shandon Baptiste 1 11 Brentford
  • Luis Sinisterra 1 14 Leeds
  • João Félix 1 15 Chelsea
  • Diego Costa 1 29 Wolves
  • Jonny 1 13 Wolves


  • Kungiyoyin da suka karbi katin gargadi da yawa guda 84:

  • Leeds United
  • Nottingham Forest
  • Wolverhampton Wanderers

  • Kungiyoyin da ke da karancin karbar katin gargadi 44:

  • Manchester City
  • West Ham United

  • Kungiyar da ta karbi jan kati da yawa guda shida a bana:

  • Wolverhampton Wanderers