You are here: HomeAfricaBBC2023 05 30Article 1776761

BBC Hausa of Tuesday, 30 May 2023

Source: BBC

Jiragen Rasha sun kwashe dare uku suna luguden wuta a kan birnin Kyiv

Jiragen yaki na Rasha | Hoton alama Jiragen yaki na Rasha | Hoton alama

An ji ƙarar fashewar abubuwa a Kyiv, kuma gine-gine da dama sun ƙone bayan da Rasha ta kai hare-hare a babban birnin Ukraine cikin dare na uku a jere.

Jami'ai sun ce tarkacen da suka faɗo ne suka haddasa gobarar, yayin da jami'an tsaron saman Ukraine suka kakkaɓo sama marasa matuƙa guda 20. Aƙalla mutum ɗaya kuma aka ruwaito ya mutu.

A Moscow, wani harin da aka kai da jirage marasa matuka daga baya ya haifar da ɓarna a wasu gine-gine, inji magajin babban birnin kasar ta Rasha.

Sergei Sobyanin ya ce "dukkan jami'an agajin gaggawa na birnin" suna wurin.

Ya ƙara da cewa "yanzu haka, babu wanda ya samu munanan rauni."

Hare-haren da aka kai a birnin Moscow sun biyo bayan wani harin da aka kai a daren jiya Lahadi a babban birnin kasar ta Ukraine.

Da take bayar da bayanan farko, hukumomin sojin Kyiv sun ce sama da jiragen Kamikaze 20 ne aka lalata a harin na baya-bayan nan.

An ce mutum daya ya mutu, uku kuma suka samu rauni sakamakon wata gobara da ta tashi a wani bene mai hawa uku da ke gundumar Holosiivskyi ta kudancin kasar.

“An lalata hawa biyu na sama, kuma kila akwai mutane a karkashin baraguzan ginin,” in ji gwamnatin a cikin wata sanarwa.

Gine-gine masu zaman kansu guda biyu sun kone tare da lalata motoci da dama a gundumar Darnytskyi - kusa da kogin Dnipro.

Magajin garin Kyiv Vitaliy Klitschko ya bayyana sabon harin a matsayin "mai girma", inda yake kira ga mazaunan garin da "ka da su bar matsugunansu".

Wannan dai shi ne hari na 17 da aka kai a babban birnin kasar tun farkon watan Mayu, ciki har da wani harin da aka kai da rana a ranar Litinin.

Shugaban kasar Volodymyr Zelensky ya yaba da kariyar tsaron saman da Amurka ta samar wa kasar Ukraine.

A cikin jawabinsa na bidiyo da yammacin ranar Litinin, ya ce sun tabbatar da "tarwatsa duk wani makami mai linzami na Rasha dari bisa dari".

Mista Zelensky ya kara da cewa, "Rasha na son bin tafarkin mugunta har zuwa karshe, za ta kai kanta ƙasa, domin mugunta ba za ta taɓa haifar da abu mai kyau ba face shan kashi.

Sai dai kuma, janar Kyrylo Budanov, shugaban hukumar leken asirin sojin Ukraine, ya yi gargadin ɗaukar matakin gaggawa kan harin na Rasha.

Sojojin Rasha sun yi nasarar kai wasu hare-hare, ciki har da wani a kan sansanin sojin sama inda aka kai hari a wasu yankuna na Ukraine.

A ranar litinin, hukumomi a yankin Khmelnysyi da ke yammacin ƙasar sun ce an lalata jiragen sama biyar a wani wurin da sojoji suke.

Hukumar ta kara da cewa yanzu haka ana gyaran titin jirgin da ke wurin, ba tare da bayar da wani karin bayani ba.

Rundunar sojin kasar Rasha ta bayyana cewa, an kai hari kan dukkan wuraren da aka nufa a lokacin hare-haren baya-bayan nan da ta kai a birnin Kyiv da sauran garuruwan Ukraine.

Ba a tabbatar da ikirarin da bangarorin da ke fada da juna suka yi ba. Rasha - wacce ta kaddamar da cikakken mamayar a watan Fabrairun 2022 - tana amfani da jirage marasa matuka na Kamikaze da kuma makamai masu linzami iri-iri.

Masu sharhi sun ce Moscow na neman raunana tsaron Ukraine gabanin kai farmakin da ta dade ana sa ran ta aiwatar.

Ukraine dai ta kwashe watanni tana shirin kai hare-hare. Amma tana buƙatar lokaci mai yawa domin horar da sojoji da kuma karbar kayan aikin soji daga ƙasashen yamma.