You are here: HomeAfricaBBC2021 05 04Article 1250263

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Neymar, Abraham, Kane, Grealish, Keita, Alaba

Neymar Jnr dan wasan PSG Neymar Jnr dan wasan PSG

Darektan wasanni na Paris St-Germain Leonardo na nuna shakku idan dan wasan gaba na Brazil Neymar, mai shekara 29, zai sabunta yarjejeniyar ci gaba da zamansa a kungiyar ta Faransa. (Jaridar Marca).

Tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United Roy Keane yana ganin in dai har kungiyar na son ta kalubalanci gogayya da abokkiyar hamayyarta Manchester City a kaka mai zuwa to ya kamata ta dauki dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane, mai shekara 27 da abokin wasansa a tawagar Ingila Jack Grealish mai shekara 25 da ke Aston Villa (Tashar Sky Sports)

Kociyan Manchester City Pep Guardiola ya ce, kungiyar ba wurin zuwan duk wani dan wasa ba ne da ba ya son a rika sauya masa wurin da yake taka leda a fili ba. (Jaridar Manchester Evening News)

Kociyan West Ham David Moyes ya ce kungiyar za ta shiga kasuwa domin nemo dan wasan gaba a bazaran nan, amma za ta fita daga zawarcin dan wasan gaba na Ingila da kuma Chelsea Tammy Abraham mai shekara 23 idan farashinsa ya kai fam miliyan 45. (Jaridar Football London)

Darektan horod da wasa na AC Milan Paolo Maldini ya ce kungiyar za ta dakatar da tattaunawa kan tsawaita kwantiragin 'yan wasa, bayan da rahotanni suka ce magoya baya sun yi wa mai tsaron ragar kungiyar kuma golan Italiya, Gianluigi Donnarumma mai shekara 22 wanda kwantiraginsa zai kare a bazaran nan, gatse-gatse.(Jaridar Ansa daga Mail)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp y ace yana ganin dan wasan tsakiya Naby Keita, dan kasar Guinea mai shekara 26, zai dade ana damawa da shi a kungiyar nan gaba. (Jaridar Mail)

Tsohon golan Holland kuma babban jami'in kungiyar Ajax Edwin van der Sar ya ce zai yi wa tsohuwar kungiyarsa Manchester United aiki amma dai zuwa yanzu ba a yi masa maganar maye gurbin mataimakin shugaban kungiyar ba mai barin gado Ed Woodward. (Jaridar ESPN)

Tottenham na sha'awar sayen dan wasan gaba na gefe dan Brazil Rodrigo Varanda, kuma tuni an fara tattaunawar farko kan dan wasan mai shekara 18 na kungiyar Corinthians. (Jaridar Sun)

Dan bayan Austria David Alaba, mai shekara 28, zai rika karbar albashi kusan Yuro miliyan 12 da Sergio Ramos ke karba a Real Madrid idan ya koma kungiyar ta Sifaniya, bayan kwantiraginsa ya kare da Bayern Munich. (Jaridar Fabrizio Romano, daga AS)

Fulham ta fara duba dan wasan gaba na Peterborough United Siriki Dembele, mai shekara 24, wanda kuma Rangers da Celtic da Crystal Palace ke sha'awarsa. (Jaridar Football Insider)