You are here: HomeAfricaBBC2021 05 04Article 1250284

BBC Hausa of Tuesday, 4 May 2021

Source: BBC

Boko Haram: Abin da ya sa za a baza jami'an tsaro kan dokuna da babura domin kare Abuja

Ana mawiyancin hali game da tsaro a wasu jihohin Najeriya Ana mawiyancin hali game da tsaro a wasu jihohin Najeriya

Rundunar 'yan sanda a Abuja, babban birnin tarrayyar Najeriya ta ce za ta baza jami'anta a kan babura da dawaki domin tattaro bayanan sirri kan masu aikata laifuka.

Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce jami'anta za su shiga lungunan da miyagun mutane ke iya fakewa kuma suke da wuyar zuwa da mota.

Ta dauki wannan mataki ne bayan wani rahoto da aka sanya a shafukan sada zumunta ya nuna cewa 'yan Boko Haram sun kai hari a wani yanki na birnin tarayyar.

Sai dai kwamitin tsaro na hadin gwiwa a babban birnin ya ce rahoton na bogi ne.

Sanarwar da mai magana da yawun rundunar ASP Mariam Yusuf ta fitar ta ce sun fitar ta ce shugabannin rundunonin tsaro na yankin sun yi wani taro inda suka fito da sabbin dabarun yaki da miyagun laifuka domin shawo kan damuwar da ake nunawa kan yanayin tsaro a babban birnin kasar.

A cewarta hakan ne ya sa za a bai wa jami'an tsaro damar hawa dokuna da babura domin yin sintiri a lunguna da sakunan birnin.

A kan haka ne hukumomin a babban birnin tarayyar ke kiran ga mazauna birnin na su kwantar da hankulansu.

Malam Abubakar Sani, kakakin ministan birnin tarayyar Muhammad Musa Bello, ya shaida wa BBC cewa "rahotanni da ke cewa wata kungiya na son kawo hari a Abuja ba gaskiya be, kuma jami'an tsaro suna kan kyakyawan bincike kuma suna lura da yadda abubuwa ke faruwa."

Ya kara da cewa an dauki karin matakan tsaro a birnin kuma ba a san ranar da za a sassauta su ba.

Wannan dai na zuwa ne kusan mako daya bayan da gwamnan jihar Naija mai makwabtaka da Abuja, Abubakar Sani Bello, ya yi gargadin cewa mayakan na Boko Haram sun kwace wani yanki a jiharsa.

A cewarsa tazarar yankin da birnin na Abuja ba ta wuce tafiyar awa biyu ba.

Daruruwan mutane ne dai suka mutu a birnin na Abuja da kewayen a cikin hare-haren bama-bamai da mayakan Boko Haram suka yi ta kai wa tsakanin shekarun 2011 da 2015.