You are here: HomeAfricaBBC2022 10 20Article 1646858

BBC Hausa of Thursday, 20 October 2022

Source: BBC

Zanga-zanga ta ɓarke a N'Djamena

Wasu yan zanga zanga Wasu yan zanga zanga

Rikici ya ɓarke a ƙasar Chadi bayan da 'yan sanda suka yi taho-mu-gama da masu zanga-zanga a N'Djamena, babban birnin ƙasar. Babu tabbas kan adadin waɗanda suka rasu amma gommai sun ji rauni bayan da jami'an tsaro suka harba barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu bore da ke yin kira a gaggauta mayar da ƙasar kan tafarkin demokradiyya. An tabbar da rasuwar wani ɗan jarida, yayin da aka wuce da waɗanda suka ji rauni zuwa asibitin Union. Masu zanga-zanga sun ƙona tayoyi sannan suka rufe manyan tituna a babban birnin ƙasar, duk da cewa gwamnati ta haramta zanga-zangar. Ƙasar Chadi ta kasance kan siraɗi tun bayan kashe shugaba Idriss Deby a watan Afrilun 2021 lokacin da ya ziyarci dakarunsa da ke yaƙi da 'yan tawaye. Jami'an tsaro sun far ma kungiyoyin farar hula da ke adawa da mulkin soji lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama a yayin da gwamnatin Faransa ke goyon bayan gwamnatin rikon ƙwarya a Chadi.