You are here: HomeAfricaBBC2022 10 20Article 1646855

BBC Hausa of Thursday, 20 October 2022

Source: BBC

Gwamnatin Kogi ta kai kamfanin Dangote ƙara

Alhaji Aliko Dangote Alhaji Aliko Dangote

Gwamnatin jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya ta shigar da ƙarar kamfanin Dangote kan batun wanda ke da mallakar kamfanin siminti da ke Obajana a jihar. Babban mai taimaka wa gwamnan kan yaɗa labarai Mohammed Onogu, ya tabbatar wa da BBC batun, inda ya ce sun shigar da ƙarar ne a ranar Laraba a gaban babbar kotun jihar da ke Lokoja. Mista Onugu ya ce gwamnatin na fatan kotu za ta yi duba a tsanake kan yarjejeniyar da ke tsakanin kamfanin Dangote da jihar Kogi da aka cimma ranar 30 ga watan Yulin 2002 da kuma ran 14 ga Fabrairun 2003. Sai dai har yanzu kamfanin Dangoten bai ce komai ba kan batun A makon da ya gabata ne gwamnatin jihar Kogi ta rufe kamfanin simintin bisa zargin cewa bai bi ƙa'ida ba wajen mallakar hannun jarinsa. Sai dai a martanin da kamfanin Dangote ya yi tun a lokacin, ya ce ya zuba jari a kamfanin simintin na Obajana, kuma ya bi dukkan ƙa'idoji kafin ya fara harkar siminti a jihar. A cikin ƙarar da gwamnatin jihar ta shigar, ta nemi kotun da ta soke yarjejeniyar bisa hujjar cewa ba ta cika sharuɗɗanta ba, waɗanda su ne ginshiƙin ingantaccen kwantiragi. Gwamnatin jihar na kuma son kotu ta hana kamfanin Dangote cin gajiyar riba ko samun wata dama daga yarjejeniyar ta 2002 da 2003, saboda rashin bai wa gwamnatin Kogin wasu muhimman bayanai kan matsayarta a kan yarjejeniyar. Kazalika tana so a soke dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla ɗin.