You are here: HomeAfricaBBC2023 08 11Article 1823291

BBC Hausa of Friday, 11 August 2023

Source: BBC

Yadda za ku shigar da korafi idan WAEC ta riƙe muku jarrabawa

Fauziyyah Hassan Haruna Fauziyyah Hassan Haruna

Hukumar shirya jarrabawar kammala Sakandire ta Afirka ta Yamma, WEAC, ta ce ta rike sakamakon jarrabawar dalibai fiye da 260 kan zargin satar jararabawa.

To sai dai hukumar ta tanadi wani wuri na musamman a shafinta na intanet da dalibai za su iya shigar da korafinsu kan rike musu jarrabawar ga hukumar.

Haka kuma shi ma dalibin da yake ganin an rage masa maki a jarrabawar, zai iya shigar da nasa korafin domin hukumar ta gudanar da bincike.

Da zarar dalibi ya shigar da korafin hukumar za ta gudanar da bincike domin sanar da shi ainihin abin da ya sa ta rike masa jarrabawar.

A wannan bidiyon, mun kawo muku matakan da za ku bi domin gano hakikanin abin da ya sa hukumar ta rike muku sakamakon jarrabawar.