You are here: HomeAfricaBBC2022 11 06Article 1657610

BBC Hausa of Sunday, 6 November 2022

Source: BBC

Yadda taurari suka fito da fina-finan India a duniya

Tutar Indiya Tutar Indiya

Fina-finai na yin tasiri da kuma karfafa mana guiwa ta hanyoyi da dama ta yadda ba wani fanni na adabi da ke yin haka kamar fim, wanda shi fim yana nuni ne da abin da ya shafe mu gaba daya da kuma burin daidaikun mutane. Kuma babu ta inda sinima take fitowa tare da nuna irin buri da soyayya da kuma rikici na mutane kamar ta fim - kamar yadda Indiya ta yi fice. Harkar fina-finan Indiya wato Bollywood, wadda taa kasance hanyar cimma wannan buri, a kodayaushe kan yi nazarin irin halin da kasar ke ciki daga nan sai a fito da wani fim wanda al'ummar Indiya za su so su kalla. Wannan ne ya sa labaran da fina-finan Indiya ke fitowa da su ta sinima ke nuna wa duniya abin da Indiya ke ciki - yadda take a baya da kuma abin da ta zama. Labarai da dama kamar na rayuwar yau da kullum ta iyalan wani gida da labaran soyayya da na ramuwar-gayya labarai ne da aka sani a duk duniya wadanda kuma suke ci gaba da wakana a rayuwar jama'a. Wasu kuma kamar na haihuwar tagwaye masu kamanni daya da suka rabu tun haihuwa, wadanda aka saba da su bayan rabuwar Indiya da pakistan, sun bace sakamakon lokacin da kuma sauyin al'amuran rayuwa. To amma akwai salon fim din da ya juri lokaci wanda har yanzu yana cin zamani, wannan nau'i kuwa shi ne wasan kwaikwayo na Indiya. Tun bayan bayyanar fim din darekta kuma mai shirya fim na Indiya na farko Dadasaheb Phalke wato Raja Harishchandra a 1913, marubuta da masu bayar da umarni a fim suke ta bullo da tarihi da kissoshi su hada labarai masu daukar hankali a kan sarakuna da sarauniyoyi. Irin wadannan labarai masu daukar hankali da ake kawata su a gabatar da su a fim, inda ake nuno maza sanye da dogayen riguna a kan dawakai da giwaye suna jagorantar mayaka a fagen-daga, ga takubba da masu ana ta fafata yaki domin kare martaba ko wata soyayya ko masarauta a kullum suna burge mu. Muna jin dadin kallonsu a lokuta na rashin tsaro da rashin kwanciyar hankali saboda har kullum suna nuna mana tare da tabbatar mana cewa karya fure take ba ta 'ya'ya. Duk yadda tafiya ta yi tafiya alheri ya fi mugunta. A baya-bayan nan fina-finan Indiya na Bollywood sun koma waiwayen baya sosai, inda ake shirya fina-finai na yaki da takubba kamar yadda aka yi a zamanin da, inda za ka ga mazaje sanye da dogayen riguna. Na kwanan nan shi ne fim din Brahmastra, wanda yake da taurarin fim irin su Ranbir Kapoor da Alia Bhatt da Akshay Kumar da Samrat Prithviraj. To amma fa a yanzu wani abu ya sauya. A wancan zamanin na da taurarin fina-finan Indiya da suke sanya dogayen riguna, suna fita ne a matsayin mutane masu daraja da kamala masu so da kaunar soyayya, amma yanzu sababin haka suna yada kiyayya ne. An yi ta nuna fim din kissar rayuwar Prithviraj Chauhan, wani sarkin Indiya wanda ya yaki sojojin mamaya na Muhammad Ghori na Afghanistan a shekarar 1191. Fim din ya dauki hankalin jama'a sosai saboda irin jarumtar da mayakin sarkin ya nuna, kan yadda ya kare masarautarsa, ba kuma wannan kadai ba har ma da yadda ya kwace Samyogita, matar da yake kauna, a gaban mahaifinta wanda bai amince da wannan soyayya ba. To amma salon yadda aka gabatar da wannan labari a fim din Akshay Kumar ya saba da yadda ake yi fim a da. Fim din Samrat Prithviraj, wanda daya daga cikin manya kuma kamfanonin hada fim da aka fi so Yash Raj Films, suka yi an shirya shi ne kan abin da ya shafi yada manufa ta addinin Hindu. A fim din ana yawan nuno launin tutar kishin kasa ta 'yan Hindu. Maganganun da ke cikin fim din yawanci na nuna wariya ne da kishin Hindu. To amma babban abin da ya fi ban takaici shi ne asalin Prithviraj Chauhan ba Indiya ba ne. Addinin Hindu ne.   Samun 'yancin kai na India Indiya wadda ta samu 'yancin kai a 1947 bayan rikicin da aka zubar da jini kan bambancin addini ta zabi ta zama kasar da ba ruwanta da addini. Kuma harkar fina-finanta ta rike tare da mutunta hakan tsawon shekara 70. Babban misalin yadda Indiya ta gabatar tare da nuna wa duniya tarihinta a da, kan gwaraza da miyagunta shi ne a fim din Sikander na Sohrab Modi na 1941. Wannan fim na Sikander an tsara shi ne kan rayuwar zamanin shekarun 327, a kan sarkin Girka, Alexander, da yakin da ya fafata da wani sarkin Indiya, Puru ( wanda aka fi sani da Porus a littattafan Girkawa).  Duk da cewa fim din ya ta'allaka ne a kan Porus, tare da gabatar da Alexander a matsayin makiyi wanda ya wajaba a kawar da shi ta ko halin kaka. An gabatar da shi a matsayin mutum mai girma da mutunci wanda ya san ya kamata, da matar da yake kauna da malaman da yake girmamawa sosai da kuma dakaru da ke masa biyayya. Duk da yadda aka tsara fim din da salon kishin kisa, an gabatar da yaki tsakanin Alexander da Porus a matsayin fada tsakanin mutane biyu gwaraza da ke mutunta juna. Kusan duk bayan shekara goma kuma har 2017, Indiya na fitowa da fina-finai fitattu inda mazaje masu dogayen riguna ke fada a fagen daga domin soyayya ko kare martaba. Dukkanninsu 'yan Indiya ne duk da bambancin addinin da za a iya samu a tsakaninsu. Kuma miyagun sun yi kaurin suna ne saboda miyagun abubuwan da suke yi da mummunar manufarsu, amma ba wai saboda abin da suke bautawa ba. Bayan samun 'yancin kai na India Shekarun 1950 lokaci ne na gina kasa da samar da masana’antu da kuma fata. Fina-finan Indiya da aka yi a lokacin yawanci sun karkata ne ga jigo na zamntakewa da kuma ra’ayin siayasa mai sassauci na kawo sauyi. Yawancin fina-finan sun shafi auren dole da soyayyar da ta jibanci al’adar nan ta kasar ta nuna bambanci da wariya ga wani rukunin jama’a a kasar ta Indiya. Fim din Aan na darekta Mehboob Khan, wanda ya fito da taurari Dilip Kumar da Nadira, (Bayahudiya), fim ne a kan yadda wani talaka yake son wata gimbiya da kuma yaki a kan sarauta. Haka kuma sa karin wasu shekaru talatin, daga shekarun 1960 zuwa na 1970 har zuwa shekarun 1980, fina-finan zaratan taurari irin su Amitabh Bachchan na matasa da ke fada a kan soyayya sun ci gaba da mamaye harkar fim din a Indiya. Sai dai an samu dan sauyi, inda a wannan karon karuwar da ke mu’amulla da manyan mutane masu iko ko attajirai ita ma ta samu wuri a harkar fim din, inda aka samu manyan taurari da suka fito a fina-finai daban-daban, kamar su Meena Kumari (Pakeezah da Chitralekha), Vyjayanthimala (Amrapali) da Rekha (Umrao Jaan). A irin wadannan fina-finan wannan mace takan bayyana abin da take bukata karara, inda take kalubalantar mutane masu matsayi da al’adar wariya har ma da manyan shugabannin iyali. A fim din K. Asif’ Mughal-e-Azam na 1956, daya daga cikin fitattun fina-finan Indiya  na wasan kwaikwayo, ‘yar rawar dandali Anarkali, wadda Madhubala ta fito a matsayin ta fito fili taa bayyana soyayyartaa ga yarima Salim, (wanda daga bisani ya sama sarkin-sarakuna) duk da cewa sarkin-sarakuna Akbar bai amince ba. Mai rawar ta bayyana sakon nata ne ta waka, Jab pyaar kiya toh darna kya (Me ya sa kake tsoro idan kana soyayya?) Wannan wani lokaci ne na bunkasar fina-finan Indiya zamanin, wanda har yanzu ba a samu wanda ya wuce shi ba. Akwai wasu fannonin da wadannan mazaje masu dogayen riguna ke bayyanawa a fina-finan na Indiya.  Fim din marubuci kuma darekta Satyajit Ray, Shatranj Ke Khiladi (Masu wasan dara), wanda  Richard Attenborough ya fito. Fim din ya kasance yana nuna irin tarihin abin da ya wakana lokacin da Turawan Birtaniya  ke kokarin kama wata masarautar Indiya ta Awadh daga hannun sarkinta, Wajid Ali Shah, sarkin Indiya na  India na Mughal na karshe. Mutumin da ya yi fice wajen al’ada, Wajid Ali Shah ya yi suna wajen yin rawa a lokutan  bukukuwan addinin Indiya, inda yake sa kaya na kawa da zobuna da awarwaro iri-iri. A kan wannan doron ne aka yi fim din 1977 wanda ya kunshi labarin mutane biyu masu kamala — Mirza Sajjad Ali da Mir Roshan Ali — mutanen sun kamu da wasan dara sosai, ta yadda ta kai har lokacin da iyalansu ke cikin wahala kuma masarautar na neman fadawa hannun Turawan Biortaniya su ba abin da ya dame su illa wasansdu na dara. Fim din Ray kamar duk wani fim na wannan lokacin — Junoon ( na 1978, wanda Shashi Kapoor da Nafisa Ali suka fito) da 36 da Chowringhee Lane ( na 1982 wanda ya sa, Jennifer Kendal, ta ci kyauta) — suna nuna irin yadda siyasar Indiya ta kunshi akidu daban-daban a fim da kuma a rayuwar gaske. Taurarin fina-finan sun hada da mabiya addinai daban-daban kama da ga Parsi da Hindu, da Kiristoci da Musulmi da ‘yan Sikh da kuma Turawan Birtaniya. Hatta su kansu masu aikin hada fina-finan sun kunshi mabiya wadannan addinai da sauransu, inda kuma suke magana da harsuna daban-daban kama daga Indiyanci da Urdu da Ingilishi. An rika yin fina-finan yawanci a Awadh ko Lucknow ko Faizabad a yankin tsakiyar Indiya. Ga kuma keken doki dauke da mata, wanda hakan ke nuna irin rayuwar wannan zamani da ake kira  “Ganga-Jamni tehzeeb”. An yi amfani da Ganges da Yamuna, koguna biyu na Indiya a matsayin sakaya domin nuna irin rayuwar da ake yi a lokacin ta zaman tare ta al’adun mabiya addinan Hindu da Musulmi.