You are here: HomeAfricaBBC2022 11 06Article 1657607

BBC Hausa of Sunday, 6 November 2022

Source: BBC

Waiwaye: Bayyana manufofin Kwankwaso, Kamen EFCC da tashin dala

Tutar Najeriya Tutar Najeriya

Manyan manufofin da Kwankwaso zai mayar da hankali a kansu A ranar Talatar da ta gabata ne ɗan takarar shugaban Najeriya ƙarƙashin jam'iyyar NNPP, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya ƙaddamar da manufofin yaƙin neman zabensa. Tsohon gwamnan jihar Kanon kuma tsohon Sanata a majalisar dattijan ƙasar ya ƙaddamar da kundin manufofinsa ne wanda ya ƙunshi ƙudurce-ƙudurce da hanyoyin da zai bi wajen aiwatar da su idan ya samu nasarar zama shugaban Najeriya. Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya gabatar da kundin manufofin nasa mai shafi 151 ne a wani gagarumin taro a Abuja, da  ya haɗa jiga-jigan jam’iyyar da dukkan manyan ƴan takarar jam’iyyar a matakai daban-daban a fadin Najeriya.  Ga cikakken labarain a nan EFCC ta kama ɗan takarar majalisa ɗauke da naira miliyan 326, da dala 610,500 Haka kuma a cikin makon da muke bankwana da shi ɗin ne kuma hukumar yaƙi da cin hanci da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da ɗan takarar majalisar dokokin jihar Kogi na jam’iyyar NNPP a gaban Kotu. Hakan ya biyo bayan kama ɗan takarar mai suna Ismaila Yusuf Atumeyi da tsabar kuɗi naira miliyan 326 da kuma dalar Amurka 140,500. Mai magana da yawun hukumar ta EFCC Wilson Uwujaren ya ce sun kama Atumeyi, wanda ke takarar ɗan majalisa mai wakiltar gundumar Ankpa 11 ne a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022. Farashin dala ya yi tashin gwauron zabo Tashin da farashin dala ya yi wani abu ne da ba za a iya kauce masa ba a Najeriya, saboda matsalolin da suka dabaibaye tattalin arzikin Najeriya. Daga watan Janairun 2022 da ake sayar da dala kan naira 565, zuwa wannan watan na Oktoba naira ta rasa darajarta da kashi 28, kamar yadda shafin Nairametrics’ FX da ke bibiyar darajar kudi ya bayyana. A cikin abin da ya gaza kwanaki 10, farashin dala ya karu da kusan naira 54, biyo bayan sanarwar da babban bankin kasar CBN ya fitar na sauya fasalin kudin kasar. Ga cikakken labarin a nan Rasuwar ɗan gidan Davido A ranar Litinin ne dai aka wayi gari da labarin rasuwar dan gidan shahararren wamaƙin nan na Najeriya Davido, wato Ifeanyi Davido, sakamkon nutsewa da ya yi a wajen ninƙaya da ke gidansu. Rundunar 'yan sandan jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ce ta gayyaci mutane takwas masu hidima a gidan shahararren mawaƙin, domin gudanar da bincike game da rasuwar ɗan mawaƙin, mai shekara uku. Ifeanyi shi ne yaro ɗaya tilo da David Adeleke (Davido) ya haifa tare da budurwarsa Chioma Rowland. Ga cikakken labarin a nan Amira Souley ce gwarzuwar gasar Hikayata ta 2022 Haka kuma a makon da muke bankwana da shi ɗin ne kuma BBC ta yi bikin karrama gwarazan gasar Hikayata ta ƙagaggun labarai, da gasar waƙoƙin cikar sashen Hausa na BBC cika shekara 65 da fara yada shirye-shirye. An yi karramawar ne a wani gagarumin biki da BBC ta shirya a Abuja babban birnin Najeriya. Taron ya samu halartar man'yan baki daga ciki da wajen Najeriya, inda masana harshe da adabin Hausawa suka gabatar da maƙaloli daban-daban. Amira Souley daga garin Maraɗi na Jamhuriyar Nijar ce ta zama gwarzuwar gasar ƙagaggun labarai ta BBC Hausa wato Hikayata ta shekarar 2022, inda ta samu kyautar dala 2000, da shaida da lambar yabo daga BBC. Sai kuma Hassana Labaran da Maryam Muhammad Sani waɗanda suka zo a matsayi na biyu da na uku. Ga cikakken labarin abubuwan da suka fara a ranar bikin