You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782197

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

West Ham ta lashe Europa Conference League

West Ham United ta dauki Europa Conference League West Ham United ta dauki Europa Conference League

West Ham United ta dauki Europa Conference League, bayan da ta ci Fiorentina 2-1 ranar Laraba a Prague.

Hakan ya kawo karshen shekara 43 rabon da kungiyar da ke buga Premier League ta dauki wani babban kofin tamaula.

Tun farko karawar ta nuna kamar sai an je karin lokaci, bayan da suke 1-1, inda Said Benrahma ya fara ci wa West Ham kwallo a minti na 62.

Sai dai kuma minti biyar tsakanin Fiorentina ta farke ta hannun Giacomo Bonaventura.

Wasan ya kusan cin karo da takaddama, bayan da aka jefi kyaftin din Fioentina, Cristiano Biraghi da robar ruwa daga wajen zaman magoya bayan West Ham.

Daf da za a tashi wasan Jarrod Bowen na West Hamm ya samu kwallo daga wajen Lucas Paqueta, haka ya dunga ja har ya zura a raga.

Nan take kocin West Ham David Moyes ya zura a guje a gefen fili, wanda yake murnar nasarar da kungiyar ta yi.

Da wannan sakamakon West Ham za ta buga Europa League a badi, kenan uku ne daga Ingila da za su buga wasannin da ya hada da Liverpool da kuma Brighton.

Kenan karo na uku a jere da kungiyar za ta buga zakarun Turai a tarihinta, wadda ta yi ta 14 a kasan teburin Premier League a bana da maki 40.

Wasa na karshe da kyaftin, Declan Rice ya yi wa West Ham, ya zama na uku bayan Bobby Moore da Billy Bonds da suka ja ragamar 'yan wasa ta lashe kofi.

Moore shine kyaftin a lokacin da West Ham ta dauki European Cup Winners Cup a 1965, shi kuwa Bonds shine kyaftin a lokacin da kungiyar ta dauki FA Cup a 1975 da kuma 1980.