You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782194

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

Newcastle da Man Utd na zawarcin Kim, Al-Hilal ba ta hakura da Messi ba

Kim Min-jae Kim Min-jae

Mai tsaron baya a Koriya ta Kudu Kim Min-jae, mai shekara 26, na gab da daidaitawa da Manchester United a kwantiragi shekara biyar daga Napoli. (Nicolo Schira)

Amma Newcastle na iya haifar da cikas a cinikin, inda yanzu haka take tattaunawa da Kim, wanda sai an biya fam miliyan 42 kan sa kafin kungiyarsa ta sake shi bisa yarjejeniyar da ya ke kai da za ta soma aiki daga 1 ga watan Yuli. (Sun)

Aston Villa ta kwaɗaitu da ɗan wasan Manchester United da Ingila Harry Maguire mai shekara 30 a wannan kaka.(Football Insider)

Villa ta kuma gabatar da tayi kan ɗan wasan Villarreal da Sifaniya Pau Torres mai shekara 26. (Mirror)

Bayern Munich ba ta cire rai kan iya jan hankalin ɗan wasan Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 29, duk da cewa magana ta yi karfi tsakaninsa da Real Madrid. (Athletic - subscription required)

Manchester City na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan RB Leipzig asalin kasar Croatia Josko Gvardiol, mai shekara 21. (90min)

Al-Hilal ba ta hakura ba domin ta sake gabatar da sabon tayin jan hankalin ɗan wasan Argentina Lionel Messi, inda a wannan karo ta ce za ta biya shi makudan kuɗaɗe har yuro miliyan 500 ya dawo kungiyarta. (Helena Condis Edo)

Ɗan wasan Uruguay Luis Suarez mai shekara 36, na shirin raba gari da Gremio domin zuwa Inter Miami tare da tsohon abokin wasansa a Barcelona Messi da kuma ɗan wasan Sifaniya Sergio Busquets, mai shekara 34. (90min)

Mai tsaron raga Inter Miami, Nick Marsman, mai shekara 32, ya ce kungiyar ta Amurka ba ta shirya karɓan Messi ba. (ESPN, via Express US)

Ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Faransa N'Golo Kante, mai shekara 32, ya kammala duk wani gwajin lafiyarsa domin soma taka leda a Al-Ittihad kan yarjejeniyar shekara biyu da aka kulla na yuro miliyan 100 a kowanne shekara. (Guardian)

Mai tsaron raga a Sifaniya David de Gea, mai shekara 32, zai yi watsi da tayi mai gwaɓi da ya samu daga Saudiyya domin ci gaba da zama a Manchester United. (Talksport)

AC Milan ta matsu kan cimma yarjejeniya da ɗan wasan Ingila Ruben Loftus-Cheek, mai shekara 27, wanda ake tunanin zai tafi Chelsea. (Football Insider)

Mai bugawa Arsenal Folarin Balogun ya kasance wanda AC Milan da Inter Milan ke hari a yanzu. (Mail)

Brighton ta shirya kashe kuɗi mai yawa wajen saye ɗan wasan Ingila da ke zaman aro daga Chelsea kan fam miliyan 40, wato Levi Colwill mai shekara 20. (90min)

Manchester United na gab da dauko ɗan wasan Monaco da Faransa Axel Disasi, mai shekara 25. (L'Equipe - in French)

Luton Town ta shiga fafutikar saye ɗan wasan Jamaica Joel Latibeaudiere, mai shekara 23, da yanzu haka yarjejeniyarsa da Swansea City ta kare. (Football Insider)