You are here: HomeAfricaBBC2023 02 17Article 1716404

BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Wani dan kallo ya amsa laifin cin zarafin golan Arsenal

Wani mutum ya amsa laifin ya kai hari ga mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale Wani mutum ya amsa laifin ya kai hari ga mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale

Wani mutum ya amsa laifin ya kai hari ga mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale, lokacin karawa da Tottenham a Premier a watan jiya.

An hauri Ramsdale da kafa a bayansa, bayan da Gunners ta yi nasarar cin Tottenham 2-0 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 15 ga watan Janairu.

An gurfanar da Joseph Watts, mai shekara 35 daga Hackney a gaban kotun majistare, wanda ya amsa ya ci zarafin mai tsaron ragar Arsenal.

Ya kuma amsa cewar ya jefa kwandala hudu cikin fili a wasan na hamayya.

Ramsdale ya taka rawar gani a wasan da Gunners ta doke Tottenham 2-0 a fafatawar hamayya ta kungiyoyin birnin Landan.

Ya sanar da kotun cewar ya ci zarafin golan a lokacin da aka tashi wasan , bayan da Ramsdale ke kokarin daukar kayan da ya ajiye a gefen raga.

Watts mai goyon bayan Tottenham ya sauko daga benen 'yan kallo a guje ya haura shinge, sannan ya yi wa Ramsdale kafa a baya.