BBC Hausa of Friday, 17 February 2023

Source: BBC

Wani dan kallo ya amsa laifin cin zarafin golan Arsenal

Wani mutum ya amsa laifin ya kai hari ga mai tsaron ragar Arsenal, Aaron Ramsdale, lokacin karawa da Tottenham a Premier a watan jiya.

An hauri Ramsdale da kafa a bayansa, bayan da Gunners ta yi nasarar cin Tottenham 2-0 a babbar gasar tamaula ta Ingila ranar 15 ga watan Janairu.

An gurfanar da Joseph Watts, mai shekara 35 daga Hackney a gaban kotun majistare, wanda ya amsa ya ci zarafin mai tsaron ragar Arsenal.

Ya kuma amsa cewar ya jefa kwandala hudu cikin fili a wasan na hamayya.

Ramsdale ya taka rawar gani a wasan da Gunners ta doke Tottenham 2-0 a fafatawar hamayya ta kungiyoyin birnin Landan.

Ya sanar da kotun cewar ya ci zarafin golan a lokacin da aka tashi wasan , bayan da Ramsdale ke kokarin daukar kayan da ya ajiye a gefen raga.

Watts mai goyon bayan Tottenham ya sauko daga benen 'yan kallo a guje ya haura shinge, sannan ya yi wa Ramsdale kafa a baya.