You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782188

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

Tagwayen da likitoci suka ce ba za su wuce shekara bakwai ba sun kai 18

Sam da Alex Bolton | Rainbow Hospice Sam da Alex Bolton | Rainbow Hospice

Tagwayen da aka ce ba za su wuce shekaru bakwai ba, sun yi bikin cika shekaru 18 da haihuwa.

Sam da Alex Bolton, da ke a ƙasar Birtaniya, an haife su suna fama da wata cuta da ta shafi lakkar ƙashin baya, lalura ce ta gado wadda ke sa jikin mutum ya zama babu karfi har ya kasa mosti.

Mahaifiyarsu, Sarah Wilson, ta ce ta samu bayani kan cutar ƴaƴan nata ne a lokacin da suke da watanni 18 kacal.

Alex ya ce shi da Sam sun yi farin cikin shiga babi na gaba a rayuwarsu.

Ms Wilson ta ce, "babu shakka cika shekaru 18 wani babban ci gaba ne ga ko wane matashi amma idan zan yi la`akari da hasashen da aka yi a lokacin da aka gano cutar, zan ce Sam da Alex sun zarce duk wani abin da na yi tunani a wancan lokacin.

Ta ce `yan biyun-wadanda ke amfani da keken guragu, waɗanda ake tallafa musu wajen cin abinci da kuma kula da kansu sun kasance suna cikin farin ciki.

"Ba kasafai suke yin ƙorafin rashin lafiyarsu ba," in ji ta.

"A ko da yaushe muna ƙoƙari mu mayar da hankali kan abin da za su iya yi tare da ɓata lokaci a kan abin da ba za su iya yi ba."

`Yan biyun sun yi bikin zagayowar ranar haihuwarsu a ranar Lahadi, inda aka tara ƴan'uwa da abokan arziƙi kusan mutum 60.

A halin yanzu suna kammala kwas na shekaru biyu a Kwalejin Derby kuma suna shirin yin karatun aikin jarida a Jami'ar Derby daga Satumba.

Burinsu shi ne su zama masu gabatarwa a talabijin.

Sam ya ce: "Lokacin da aka fara gano muna da cutar, an gaya mana cewa ba za mu wuce shekaru bakwai ba kuma hakan ya tsoratar da mahaifiyarmu."

Alex ya ce "Wannan babban ci gaba ne a gare mu kuma ko yaushe zai kasance babban lamari ne a rayuwarmu.

"Yana nuna babi na gaba na rayuwarmu kuma muna matukar farin ciki."

Ms Wilson ta ƙara da cewa za ta yi tattaki domin tara kuɗaɗe gidauniyar da ke tallafawa iyalin ta tun lokacin da yaran ke da shekaru uku.