You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782191

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

Shekara 25 da rasuwar Janar Sani Abacha

Janar Sani Abacha Janar Sani Abacha

An cika shekara 25 da rasuwar tsohon shugaban kasar Najeriya na mulki Soja, Janar Sani Abacha.

A ranar 8 ga watan Juni 1998 janar Sani Abacha ya rasu.

Rasuwarsa a wancan lokacin ta girgiza jama'a musamman ganin cewa bai kwanta jinya ba.

Marigayin ya rasu ne a jajibirin ranar da ya gudanar da ayyukansa kamar yada ya saba a matsayinsa na kwamandan askarawan Najeriya.

Uwargidansa Maryam Abacha ta ce iyalinsa na yi wa marigayin adu'o'i a duk ranar zagayowar mutuwarsa.

"Muna adu'o'i da mu da mutanen gida da limamanmu na gida, mu na fida’u, mu na mi shi adu'o'i" a cewarta.

Hajiya Maryam Abacha ta kuma ce rayuwarsa da iyalinsa ta sha banban da aikinsa na soja.

A cewarta marigayin mutum ne mai son yin raha da iyalinsa da kuma motsa jiki.

"Zai tashi da safe ya yi adu'a irinta adininsa, ya shirya ya tafi wurin aiki kuma ya dawo ya ci gaba da harkokinsa", in ji ta.

Rayauwar marigayi Sani Abacha

A ranar 20 ga watan Satumba ta shekarar 1944 aka haifi Sani Abacha a Kano .

Ya halarci kwalejin horar da Sojoji ta Najeriya da ke Kaduna.

Tsawon shekarun da ya yi kan mulki

Abacha ya yi mulki a matsayin shugaban kasa kuma babban kwamadan sojojin tarayyar Najeriya daga 1993 zuwa 1998.

Rawar da ya taka a tattalin arzikin Najeriya

A karkashin mulkinsa ne asusun kuɗaɗen wajen kasar ya karu daga dala miliyan 494 a 1993 zuwa dala biliyan 9.6 a tsakiyar 1997 sannan ta rage bashin da ake bin kasar daga dala biliyan 36 a 1993 zuwa dala biliyan 27 a 1997.

Mutuwarsa

A ranar 8 ga watan Yunin 1998, janarar Abacha ya rasu a fadar shugaban kasa.

Gwamnatin kasar ta bayyana bugun zuciya a matsayin abinda ya yi sanadin mutuwarsa, sai dai jami'an diflomasiya na kasashen waje, ciki har da manazarta leken asirin Amurka, sun ce mai yiwuwa an sanya masa guba ne.

Ga wasu ‘yan Najeriya marigayi Abacha shugaban kasa ne da ya raka rawar gani wajan kawo ci gaba ga kasar yayin da wasu kuwa na kallonsa a matsayin shugaba mai mulki kama karya.