You are here: HomeAfricaBBC2021 04 19Article 1237201

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Najeriya da Nijar: Hotunan ganawar Buhari da Bazoum a Abuja

A ranar Litinin 19 ga watan Afrilun 2021 ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin takwaransa sabon shugaban Nijar Mohamed Bazoum a fadarsa da ke Abuja.

Fadar shugaban Najeriya ta sanar isowar sabon shugaban kasar na Nijar a shafukanta na sada zumunta, yayin da ita kuma fadar shugabn kasar Nijra ta wallafa hotunan ziyarar.

Ziyarar dai ta mayar da hankali ne kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro da take neman addabar kasashen biyu.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce "wajibi ne" kasarsa da makociyarta Nijar su hada hannu wajen tabbatar da tsaron kasashen biyu.

Buhari wanda ya karbi bakuncin takwaransa na Nijar Mohamed Bazoum a Abuja ranar Litinin, ya ce hakan ya zama dole ganin yadda matsalar tsaro ke tilasta wa wasu 'yan Najeriya tserewa cikin Nijar.

"Za mu yi dukkan mai yiwuwa wajen tabbatar da tsaron kasashenmu," a cewar Buhari cikin wata sanarwa da mataimakinsa na kan kafafen yada labarai, Femi Adesina, ya fitar.

"Ganin cewa wasu 'yan Najeriya na guduwa cikin Nijar saboda hare-haren 'yan ta'adda, hakan nay a nuna cewa akwai bukatar mu hada hannu domin fuskantar kalubalen tare."

A nasa bangaren, Shugaba Bazoum ya ce ya zabi ziyartar Najeriya ne a karon farko "saboda Najeriya da Nijar na da muradi guda daya kuma mai matukar amfani da kuma kyakkyawar alaka".

Manyan jami'an gwamnatin Najeriya ministoci da ma wasu gwamnoni na cikin waɗabda suka taya Shugaba Buharin tarbar Shugaba Bazoum.