You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1218208

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: BBC

Mozambique: Masu ikirarin jihadi sun hallaka gomman mutane

Masu ikirarin jihadi sun kai hari a garin Palma da ke arewacin Mozambique Masu ikirarin jihadi sun kai hari a garin Palma da ke arewacin Mozambique

Hukumomin tsaro a Mozambique sun sanar da mutuwar gomman mutane, a wani hari da masu ikirarin jihadi suka kai a garin Palma da ke arewacin kasar.

Hukumomin su ce bakwai daga cikin mutanen sun rasa rasu ne yayin da suke kokarin tserewa daga otal din da maharan suka rutsa, tun ranar Laraba.

Sai dai kuma rahotanni sun ce an samu nasarar kubutar da wasu daruruwa da suka hada da 'yan kasar ta Mozambique da kuma baki 'yan kasashen waje.

Tun a ranar Laraba ne maharan suka rika kai hare-hare a wannan yanki na garin na Palma da ke arewacin Mozambique.

Wasu da lamarin ya rutsa da su, sun bayyana yadda suka samu suka buya, yayin da ake artabu tsakanin dakarun tsaron kasar da mayakan,ana kokarin kubutar da su ta jirgin ruwa, a bakin tekun da suka ce baa bin da ake gani sai gawarwakin mutane ba kawuna.

Shafukan yada labarai ta intanet na zaratan sojin ruwan kasar sun rika nuna tarin jiragen ruwa a kusa da garin na Palma, da kuma tashar ruwa ta garin Pemba da ke kudu, yayin da mutane ke ta kokarin tsira ko ta halin kaka daga hare-haren - a cikin tekun ko ina jiragen ruwa ne kama daga na dakon kaya, da na daukar fasinja da na wasanni da shakatawa da kuma na janwe.

Wani kakakin ma'aikatar tsaron Mozambique din, Omar Saranga, da yake jawabi a babban birnin kasar Maputo, ya ce daruruwan mutane sun samu sun tsira daga farmakin, cikinsu har da ma'aikata 'yan kasashen waje da ke aikin hakar iskar gas;.

Ya ce "a cikin kwanki ukun da suka gabata, dakaru da sauran jamian tsaron kasar sun gudanar da ayyukan tsaro, wanda da farkoo suka mayar da hankali wajen ceto daruruwa jama'a, 'yan kasa da kuma 'yan waje, da kuma kare 'yan kasa da kayayyakinsu."

Mutane da dama sun shafe kwana hudu an rutsa su a otal. A duk lokacin da suka yi kokarin tserewa, maharan sai su bude wa motocinsu wuta, inda har suka kashe farar hula bakwai.

Kakakin ma'aikatar tsaron ya ce dakarun gwamnati na kokarin ganin sun kama maharani

Ya ce, "dakaru da jamian tsaron kasar na takaicin wannan asara da aka yi ta rayukan jama'a, kuma suna cewa za su ci gaba da kokarin yin duk abin da za su yi domin ganin sun kawar da 'yan maharan da suke tirjiya.

"Dakaru da jamian tsaron kasar sun tabbatar da mutuwar mutum bakwai, a cikin tawagar da ta bar optal din Amarula, wadda 'yan ta'addar suka yi wa kwanton bauna."

Wani dan kwangila ya sheda wa BBC cewa , da yawa daga cikin wadanda suka tsira daga otal din ta cikin tawaga, sun buya a otal din da daddare tun Juma'a, kuma an samu nasarar kubutar da su ne ranar Asabar da safe.

Ya ce bayan shi ma an kuma yi nasarar ceto mutane da dama, inda ake amfani kananan jiragen ruwa a aikin ceton.

Ya ce jama'ar yankin ne farar hula ke tsaimakawa wajen tsara aikin ceton.

Wani da ke ganin yadda aikin ke gudana ya sheda wa kamfanin dillanicin labarai na AFP cewa ya ga wani jirgin ruwa da mutane kusan 1,400 da suka isa garin Pemba, wanda ke da nisan kilomita kusan 250 kudu da garin na Palma inda aka kai harin.

Kungiyoyin agaji sun ce ana sa ran karin kananan jiragen ruwa dauke da mutanen da aka ceto daga yankin da za a kai ta tashar ruwan ta Pemba su isa da safiyar nan ta Litinin.