You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1199986

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Salah, Gerrard, Christensen, Hamsik, Ibrahimovic

'Yan ƙwallon Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane 'Yan ƙwallon Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane

"Wajibi ne" Liverpool ta rasa ɗaya daga cikin 'yan wasan gabanta a ƙarshen kakar wasa ta bana, Sadio Mane mai shekara 28, Salah mai 28, Roberto Firmino mai 29, a cewar tsohon ɗan wasan Ireland, Tony Cascarino. (Talksport)

Tsohon shugaban ƙungiyar Rangers, Dave King, ya ce ba zai yiwu ba mai horar da ƙungiyar wato Steven Gerrard ya bar ta domin ya zama kocin Liverpool a nan kusa. (Glasgow Times)

Chelsea na ƙoƙarin sake yi wa ɗan wasan bayanta kuma ɗan ƙasar Denmark mai shekara 24, Andreas Christensen, tayin sabon kwantaragi.

Ana sa ran Zlatan Ibrahimovic mai shekara 39 zai dawo da buga wa ƙasarsa ta Sweden wasanni a wannan watan. (Mail)

Tsohon ɗan wasan tsakiya na Lazio, Marek Hamsik, zai koma IFK Gothenburg. Ɗan ƙasar Slovania ya shafe lokaci yana buga tamaula a China a ƙungiyar Dalian Professional. (Expressen - in Swedish)

Ƙungiyar Millwall mai buga gasar Championship ta Ingila na son Luke McCormick mai shekara 22. (Sun)

Tsohon ɗan wasan Barcelona Xavi ya lashe kofi na farko a matsayinsa na koci bayan ya taimaka wa Al Sadd ta lashe kofin gasar QNB Stars League ta Qatar. (Marca)

Kocin Faransa Didier Deschamps ya ce bai kamata ma a riƙa tunanin Antoine Griezmann ba shi da wuri a cikin tawagar ƙasar. (beIn Sports via Sport - in Spanish)