You are here: HomeAfricaBBC2021 03 09Article 1200022

BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

James Ibori: Ayyukan da Najeriya za ta yi da kuɗaɗen da Birtaniya ta ƙwato

Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori Tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori

Biraniya ta yi alƙawalin dawo wa Najeriya da sama da fam miliyan hudu da tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori ya sace.

Najeriya da Burtaniya sun rattaɓa hannu ne kan wata yarjejeniya don mayar wa da Najeriya da kuɗaɗen.

Ministan shari'ar kasar Abubakar Malami da kuma Babbar Jakadar Burtaniya Catriona Laing ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

A 2012 ne Birtaniya ta samu tsohon gwamnan da laifin satar kuɗaden tare da yanke msa hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari.

Tsohon gwamnan, ya amsa laifi a gaban kotun ondon, bisa jerin tuhume- tuhume goma da aka yi masa na salwantar kudaden haram, da kuma hada baki domin tafka zamba.

Ana tunanin tsohon gwamnan ya saci kusan fam miliyan 50 na jihar Delta mai arzikin mai.

Wannan ne karon farko da za a dawo wa Najeriya kuɗaɗen da ƙwace da masu laifi suka sace tun yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a 2016, kamar yadda hukumomin Birtaniya suka bayyana.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta yi amfani da kuɗaden domin kammala ayyukan da take yi na raya ƙasa.

Ministan Shari'a Abubakar Malami cikin sanarwar da ya fitar ya ce majalisar zartarwa ƙarƙashin jagorancin shugaba Buhari ta amince kuɗaɗen da aka ƙwato a yi amfani da su wajen kammala ayyuka kamar haka:

Malami ya kuma ce gwamnatin Tarayya za ta yi aiki da ƙungiyoyin fararen hula don tabbatar da sa ido da kashe kuɗaɗen a hanyoyin da suka dace.

Yayin jawabinta, jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing CB ta ce, Najeriya da Burtaniya sun lashi takobin ci gaba da share hanya don sauran kasashen duniya su bi sahu wajen yakin da ake yi na murkushe cin hanci da rashawa.

Jekadiyar ta ce an ƙwato kuɗaɗen ne daga ƴan uwa da kuma wasu na hannun daman tsohon gwamnan na Delta.

Sannan ta ce wannan sanya hannun dai-dai yake da wani mataki na mayar da kason farko na ƙadarorin da aka sace a Najeriya.