You are here: HomeAfricaBBC2021 05 02Article 1248628

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: bbc.com

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar White, Abraham, Messi, Alaba, Ten Hag, Lukaku

Dan wasan gaba na Uruguay Luis Suarez, wanda ya koma Atletico Madrid daga Barcelona a bazarar da ta wuce ya shawarci dan wasan gaba na Argentina Lionel Messi, mai shekara 33, da ya ci gaba da zama a Nou Camp. (Tashar TV3 daga Sport)

Real Madrid ta shirya sanar da daukar dan bayan Austria David Alaba, mai shekara 28, wanda zai kasance ba shi da wata kungiya bayan kwantiraginsa da Bayern Munich ya kare a bazaran nan. (Jaridar Mundo Deportivo)

Dan wasan tsakiya na Arsenal, dan Ingila Bukayo Saka, mai shekara 19, ya ce bai yi wani jinkiri ko wani tunani ba kan yarda da kulla sabuwar yarjejeniya da Gunners, duk da sha'awarsa da Borussia Dortmund da Liverpool suke yi. (Jaridar ESPN)

Borussia Dortmund ta bi layin kungiyoyin da ke sha'awar sayen dan wasan baya na Brighton, kuma dan Ingila Ben White, mai shekara 23, duk da cewa Paris St-Germain da Manchester United da kuma Arsenal har yanzu suna sonsa. (Jaridar Sun)

Aston Villa ta zauna cikin shiri bayan da ta bayyana cewa Chelsea a shirye take ta karbi kusan fam miliyan 40 a kan dan gabanta na Ingila Tammy Abraham, mai shekara 23. (Jaridar Mirror)

Tottenham na son tattaunawa da Erik ten Hag domin daukarsa ya maye gurbin kociyanta da ta kora Jose Mourinho. Kociyan mai shekara 51 na sha'awar jagorantar wata sabuwar kungiya bayan shafe shekara hudu a matsayin mai horad da Ajax. (Jaridar Guardian).

To amma kuma duk da wannan labara, Spurs din har yanzu na zawarcin kociyan Leicester Brendan Rodgers, duk da cewa a ranar Laraba kociyan na Leicester ya ce ba shi da sha'awar aikin. (Jaridar Mail)

Inter Milan ta gaya wa Manchester City cewa ba ta da shirin sayar da dan wasanta nag aba, dan Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 27. (Jaridar Calciomercato ta Italiya)

Leicester za ta nemi sayen dan bayan Atalanta kuma na tawagar Jamus Robin Gosens, mai shekara 26, idan kungiyar ta samu gurbin zuwa gasar Zakarun Turai. (Jaridar Tuttomercatoweb daga Team Talk)

Inter Milan na duba yuwuwar tsawaita zaman tsohon dan bayan Ingila Ashley Young idan ta ci kofin gasar Serie A a karshen wannan makon. Amma kuma Watford ma na sha'awar daukar tsohon dan bayan mai shekara 35, da ya samu horo a kungiyar. (Jaridar Mirror)

Everton na daga kungiyoyi Premier da yawa da ke son sayendan gaban RB Leipzig, dan kasar Koriya ta Kudu Hwang Hee-chan, mai shekara 25. (Jaridar Goal)

West Ham da Newcastle na sha'awar sayen dan wasan Southampton Mario Lemina. Dan wasan na tsakiyar dan Gabon mai shekara 27, a yanzu yana zaman aro ne a Fulham kuma ana ganin kungiyar za ta sayar da shi ne a kan fam miliyan 7. (Jaridar Guardian)

Dan bayan Chelsea Andreas Christensen ya ce yana son kulla sabuwar yarjejeniya ta tsawaita zamansa a kungiyar ta Premier. Dan wasan na kasar Denmark mai shekara 25, yana cikin shekararsa ta goma ke nan a Stamford Bridge. (Jaridar Metro)

Southampton na sanya ido sosai a kan mai tsaron ragar West Brom Josh Griffiths kafin kamala daukarsa a bazara. Golan mai shekara 19 wanda ke zaman aro a kakar nan a Cheltenham na taka rawar-gani a kungiyar. (Jaridar Football Insider)

Leeds ta yi watsi da bukatar Legia Warsaw ta daukar Mateusz Bogusz, dan kasar Poland mai shekara 19, aro a kaka ta gaba. (Jaridar Football Insider)

Join our Newsletter