You are here: HomeAfricaBBC2021 05 02Article 1248625

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Game of Thrones: Abubuwa hudu da suka kamata ku sani kan sabon shirin mai suna House of Dragon

House of Dragon ne sabon shiri a Game of Thrones House of Dragon ne sabon shiri a Game of Thrones

An fara naɗar sabon shirin Game of Thrones mai suna Game of Dragon a lardin Cornwall.

Kamfanin HBO mai shirya fim din ya tabbatar da fara naɗar shirin da wasu hotuna da ya wallafa na taurarin fim ɗin suna karanta labarin shirin.

Haka kuma, ana ta yaɗa hotunan masu ɗaukar hoto da wasu taurarin shirin da ake tunanin Matt Smith da Emma D'Arcy (Gimbiya Rhaenyra Targaryen a cikin shirin) ne sanye cikin irin kayayyakin da aka saba ganisu a ciki, a Holywell Bay kusa da Newquay a lardin Cornwall na Burtaniya.

Ga abubuwa huɗu da za ku so ku sani game da shirin na House of Dragon:

1. Sabon shirin zai mayar da hankali ne kan abubuwan da suka faru shekaru 300 kafin faruwar labarin Game Of Thrones kuma zai bayar da labarin iyalin gidan Targaryen. Wato dai, maimakon ci gaban labarin Game of Thrones, House of Dragon zai duba jerin abubuwan da suka auku kafin a shiga labarin Game of Thrones.

2. Wannan shirin na dogon zango zai bi labarin littafin marubuci George RR Martin ne mai suna Fire & Blood wanda aka wallafa a shekarar 2018.

3. Ana sa rai za a fitar da shirin a shekrar 2022 a manhajar kallon fina-finai ta HBO Max a Amurka.

4. Matt Smith, wanda ya yi fice a rawar da yake takawa a shirin The Crown a matsayin Duke na Edinburgh, zai fito a House Of Dragon a matsayin Yarima Daemon Targaryen.

Kamfanin HBO ya wallafa wasu hotunan ƴan wasan ciki har da Paddy Considine suna karanta labarin yayin da suke zaune a tebura daban-daban kuma sun ba da tazara saboda cutar korona.

Ƴan wasa Steve Toussaint (The Sea Snake a cikin shirin) da Olivia Cooke (Alicent Hightower a cikin shirin) da Rhys Ifans (Otto Hightower a cikin shirin) ma na zaune a teburan.