You are here: HomeAfricaBBC2023 01 29Article 1704191

BBC Hausa of Sunday, 29 January 2023

Source: BBC

FA Cup: Brighton ta cire Liverpool 2-1

Yan wasan Brighton | Hoton alama Yan wasan Brighton | Hoton alama

Kaoru Mitoma ya ci wa Brighton kwallon da ta kayatar, ta kuma cire Liverpool daga kofin kalubale na FA a Ingila.

Ana daf da tashin wasan ne dan kasar Japan din ya ci kwallon, bayan da ya kwantar da mai tsaron bayan Liverpool din, wato Gomez.

Sati biyu kenan da Brighton ta ci yaran na Jurgen Klopp 3-0, kuma sun farke kwallon su ta farko ne ta hannun Tariq Lamptey, bayan da Harvey Elliott ya fara ci wa Liverpool.

An yi tunanin wasan zai tafi zagaye na biyu ganin cewa lokacin tashi ya kure, sai gashi Mitoma ya ci wata kwallo mai kayatarwa, da ta ba Brighton damar kai wa zagayen gaba a gasar.

Kungiyar ta Anfield ce ke rike da kofin na FA, to amma a bana tana jin jiki a gasar Ingila musamman a Premier League, inda suke zaune na tara a teburi, yayin da Brighton ke na shida.

Mitoma ne dan wasan Seagulls da ke haskawa a baya bayannan, yayin da Leandro Trossard ya tafi Arsenal, kuma ake hasashen Moises Caicedo zai bishi Gunners din.