You are here: HomeAfricaBBC2023 01 29Article 1704188

BBC Hausa of Sunday, 29 January 2023

Source: BBC

An kama 'yan sanda biyar bisa zargin kisan kai a Amurka

Hoton alama Hoton alama

Rundunar 'yan sanda ta birnin Memphis da ke Murka ta kama jami'anta biyar bisa zargin kashe Tyre Nichols, tare da soke rundunarta ta musamman mai yaƙi da laifukan kan titi ta 'Scorpion' domin maido da zaman lafiya a unguwanni, wanda aka zargi jami'anta da haddasa mutuwarsa.

Rundunar mai jami'ar 50 an ɗora mata alhakin yaƙi da muyagun laifuka a wasu sassan birnin.

To sai dai yanzu an soke rundunar bayan da aka ga jami'anta a wani bidiyo suna dukan Mista Nichols mai shekara 29, ranar 7 ga watan Janairu.

A wata sanarwa da rundunar 'yan sandan birnin ta fitar ta ce ''ta yanke shawarar soke rundunar gaba ɗaya ne domin martaba rundunar.

Iyalan mista Nichols sun yi maraba da wannan matakin a wata sanarwa da suka fitar ta hannun lauyansu, suna masu kira ga hukumomi da su yi abin da ya dace domin hukunta mutanen da ake zargi da aikata kisan gillar kan mista Nichols, domin yi wa al'ummar Memphis adalci.

A watan Oktoban 2021 ne aka ƙaddamar da rundunar domin yaƙi da aikata munanan laifuka, kamar satar mota da ayyuka masu alaƙa da 'yan daba.

Tuni dai aka kori jami'an 'yan sandan biyar waɗanda aka samu da laifin kisan na makon da ya gabata.

An kuma gabatar da su a gaban kotu ranar Alhamis inda aka tuhume su da laifin kisan kai, da wasu laifuka masu alaƙa da kisan gilla.

To sai dai lauyoyin biyu daga cikin jami'an sun ce jami'an ba su amince da laifin ba.

Ɗaruruwan masu zanga-zanga ne da suka taru a harabar shalkwatar rundunar 'yan sandan birnin Memphis suna neman sauyi a rundunar 'yan sandan wanda suka ce tana aikata zalunci a birnin da ma ƙasar baki ɗaya. 

''An soke rundunar da ta kashe Tyre'', in ji wani mai zanga-zanga da yake magana da tarho a taron jama'ar waɗanda suka tsinke da sowa.

A zantawarta da BBC ranar Juma'a shugabar 'yan sandan birnin CJ Davis ta ce an samar da rundunar 'Scorpion' ne domin magance laifukan 'yan bindiga daɗi a birnin.

To amma ta yarda cewa jami'an rundunar da suka kashe Tyre Nichols sun aikata zalunci.

''Muna auna ayyukan duka rundunonin da ke ƙarƙashinmu'' in ji ta.

''Wannan mataki ne da ya wajaba mu ɗauka. muna buƙatar yin ayyukanmu a buɗe ga jama'a''.

Da farko 'yan sanda sun ce sun tsayar da mista Nichols ne kan zarginsa da tuƙin ganganci, wanda kuma ba a tabbatar ba.

Ya mutu ne ranar 10 ga watan Janairu, a asibiti kwanaki uku bayan dukan da ya sha a hannun 'yan sandan.

Kamar sauran jami'an 'yan sandan biyar da ake zargi shi ma mista Nichols baƙar fata ne.

Rundunar 'yan sandan ta saki wasu bidiyoyi huɗu da aka naɗa daga wuraren tsayar da ababen hawa bayan faruwar lamarin ranar Juma'a, wanɗanda tsawonsu ya kai sa'a guda.

Bayan sakin bidiyoyin ne kuma aka ƙaddamar da zanga-zangar lumana a birnin, inda wasu masu zanga-zangar suka toshe manyan titunan birnin, bayan wasu da aka samu a wasu wurare a faɗin ƙasar.

Da yawa daga cikin masu zanga-zangar na riƙe da kwalaye suna neman a yi wa mista Nichols adalci, da kuma kawar da zaluncin 'yan sanda.

Magajin garin birnin Memphis ya ce daga watan Oktoban 2021 zuwa Janairun 2022, rundunar ta kama mutum 566, da ƙwace wa mutane tsabar kuɗin da suka kai dala 100,000 tare da ababane hawa 270 da makamai 253.

Ɗaya daga cikin jami'an da aka kama kan zargin kashe mista Nichols an taɓa kai shi ƙara bayan da wani mutum ya zarge shi da dukansa a lokacin da yake fursuna shekara takwas da suka gabata.