You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782233

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

Ciwon sanyi na jima'i ya tsananta a Ingila

Wani mei rike da kwaroron roba Wani mei rike da kwaroron roba

Sabbin alƙaluma sun nuna cewa Ingila na fuskantar matasalar ƙaruwar kamuwa da cututtukan sanyi na jima'i da suka hada da ciwon sanyi na 'gonorrhoea' da kuma yankan gashi wato 'syphilis', bayan sun ɗan yi sauki sakamakon shekarun da aka yi ana fama da cutar corona.

Ana bai wa mutane shawara da su rinƙa amfani da kariya wurin jima'i kuma su rinƙa zuwa ana gwada su ko suna cikin haɗarin kamuwa da cututtukan.

An samu mutane 82,592 da suka kamu da ciwon sanyi a shekarar 2022 - wato karin da kashi 50% a kan mutane 54,661 da aka samu a shekarar da ta gabace ta, in ji Hukumar lafiya ta Burtaniya.

Cutar yankan gashi kuma ta karu da kashi 15% daga 7,543 zuwa 8,692.

Rukunin shekarun da za su fi yawan kamuwa da cutar ta hanyar jima'i su ne mutanen da ke tsakanin shekaru15 zuwa 24.

Hukumar lafiyar ta bayar da shawarar cewa amfani da kwaroron roba shi ne "kariya mafi kyawu."

Alkaluma sun nuna cewa:

An yi gwaji 2,195,909 kan cututtukan jima'i - ƙarin kashi 13 daga waɗanda aka yi a shekarar da ta gabata.

Cutar Chlamydia ita ce cutar da aka fi yawan kamuwa da ita, inda aka samu mutane 199,233 da suka kamu da ita.

Kamuwa da Cutar yankan gashi ya ƙaru zuwa matakin da ya fi yawa tun shekarar 1948.

kamuwa da ciwon sanyi ya kai matakin da ba a taɓa samu ba tun da aka fara fitar da alƙaluma a 1918.

Dokta Hamish Mohammed na ma'aikartar lafiyar Birtaniya ya ce:" Cututtukan jima'i ba ƙaramin al'amari ba ne, suna iya kawo babban ƙalubale ga lafiyar jama'a da abokan zamansu."

"Kwaroron roba shi ne mafi kyawun kariya, amma idan ba ku yi amfani da shi a karo na ƙarshe da kuka sadu da sabon abokin tarayya ba, akwai bukatar yin gwaji domin gano duk wata cuta da za a iya kamuwa da ita da wuri kuma a hana wasu kamuwa da ita.

Gwaji yana da mahimmanci saboda yana yiwuwa ba za a ga alamun cututtukan a zahiri ba."

Richard Angell, Babban Darakta na gidauniyar Terrence Higgins, ya ce raguwar ayyukan kula da lafiyar jima'i na kara wa lamarin muni: "An yi matukar yanke kasafin kudin ayyukan kiwon lafiyar jima'i.

"Wannan ya ƙara ta'azzara kuma ya fito fili a lokacin ɓarkewar cutar mpox a bara, wanda ya sa asibitocin kula da lafiyar jima'i a wuraren da cutar ta fi ƙamari ba su iya gudanar da gwajin cutar HIV da sauran cututtkan jima'i ba, an kuma samu ragi wajen rigakafin cutar HIV da samun damar hana haihuwa saboda rashin waɗannan muhimman ayyuka da aka samu.

Idan har ba a tabbatar da cewa an samu kayan aikin kula da lafiyar jima'i ta hanyar samun su cikin sauƙi ba - ba za mu ga ragi cikin yadda ake kamuwa da waɗannan cututtukan ba.

Mbene ne ciwon sanyi kuma ta yaya ake kamuwa da shi?

Wannan cuta ce da ƙwayar cutar 'Neisseria gonorrhoeae' ke haifarwa.

Cutar takan yaɗu ne ta hanyar jima'i.

Alamomin kamuwa da ita na iya haɗawa da fitar ruwa mai launi daga al'aura da kuma zafi lokacin fitsari da zubar jini tsakanin lokutan haila.

Amma sau da yawa cutar ba ta nuna alamu idan ta kama farji ko dubura.

Idan ba a kula da cutar ba tana iya haifar da rashin haihuwa, da cutar kumburin kashin kugu, kuma jarirai na iya kamuwa da ita yayin da ake ɗauke da su a ciki.

Yadda ake gwajin ciwon sanyi

Ba duka cutukkan sanyi na jima'i ne ke nuna alamu ba. Akwai wurare da dama da za a iya zuwa domin yin gwaji.

Waɗansu gwaje-gwajen za a iya siya a shagon magani domin gudanar da su a gida.

Ana iya magance mafi yawan cututtukan sanyi na jima'i, ko da yake akwai waɗansu nau'ukan da ke bijire wa magungunan rigakafi - kuma yanzu ana samun bullowar wadansu nau'o'in da ke da wahalar warkarwa da ake kira "super-gonorrhea."

Wasu cututtuka, irin su HIV da makamantansu, ba sa barin jiki baki daya amma akwai magunguna da za su iya rage alamunsu.