You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782230

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

Me ya sa Japan ke sauya abin da ake nufi da fyaɗe?

Hoton alama Hoton alama

"Tun da ba zan iya neman haƙƙina ta waccan hanyar ba, shi kenan sai mutumin ya ci gaba da rayuwarsa cikin 'yanci da watayawa, abin yana min zafi," a cewar Megumi.

Sai dai mai yiwuwa ana ƙoƙarin samun canji.

Majalisar dokokin Japan a yanzu na tafka muhawara a kan wani muhimmin ƙuduri, wanda zai yi wa dokokin aukawa mutum da jima'i garambawul, irin wannan gyara shi ne na biyu kawai a cikin shekara 100.

Ƙudurin dokar na ƙunshe da sauye-sauye masu yawa, sai dai mafi girma da muhimmanci shi ne wanda 'yan majalisar ke ƙoƙarin canza yadda ake kallon fyaɗe daga "yin jima'i ta ƙarfi" ko kuma "yin jima'i babu yardar mutum" - a zahiri dai a shigar da hurumin doka cikin batun neman yardar mutum a mu'amalar jima'i tsakanin jama'a, inda har yanzu ake da raunin fahimtar hakan.

A yanzu dai dokokin Japan suna bayyana ma'anar fyaɗe ne a matsayin yin jima'i ko aikata wasu ayyukan batsa "ta hanyar tilasta mutum" da kuma "ta hanyar auka wa mutum ko razanarwa".

Ko kuma ta hanyar ci da gumin mutum "wanda ba ya cikin hayyanci ko kuma ba zai iya nuna turjewa ba".

Hakan ya saɓa da sauran ƙasashe da dama waɗanda ma'anar fyaɗe ta fi faɗi inda ta shafi har batun duk wani jima'i ko tarawa da mutum ba tare da yardarsa ba - wato dai ƙasashen da idan mutum ya ce a'a to lallai a'a ne a gaban shari'a.

Masu fafutuka sun ce taƙaita ma'anar fyaɗe da Japan ta yi, ya sa masu shigar da ƙara da alƙalai na yi wa dokar ƙuntatacciyar fassara, abin da kan janyo da wuya a iya tabbatar da adalci da kuma ci gaba da ɗabbaƙa al'adar kawo shakkun da ke zama tarnaƙi ga waɗanda aka yi wa fyaɗe ta yadda za su iya zuwa su ba da rahoto a kan abin da aka yi musu.

A wata shari'a da aka yi a Tokyo cikin 2014, ga misali, wani mytum ya tokare wata yarinya 'yar shekara 15 da bango, inda ya yi lalata da ita duk da tana nuna bijirewa.

Amma an wanke shi daga laifin fyaɗe, saboda kotu ta yanke hukuncin cewa abin da ya yi bai sa yarinyar cikin "tsananin wahalar" da za ta kasa turjewa ba.

An yi wa matashiyar kallon babbar mace saboda shekarun da mutum zai kai a shari'ance kafin ya ba da amincewa a yi jima'i a Japan, shekara 13 ne kawai.

Su ne shekaru mafi ƙaranci a cikin manyan ƙasashen duniya masu ci gaban dimokraɗiyya.

"Haƙiƙanin tsare-tsaren shari'a da hukunce-hukuncen da ake yi suna bambanta - wasu waɗanda aka yi ƙarar ba a iya samun su da laifi ko da abin da suka aikata babu yardar wadanda aka yi wa fyaɗen.

Saboda abin da aka tuhume su da shi, bai kai matakin "aukawa mutum da jima'i ko razanawar ba," a cewar Yuu Tadokoro, wani mai magana da yawun ƙungiyar Spring, ta mutanen da aka taɓa yi wa fyaɗe.

Hakan ce ta sa Megumi ta ce ba su kai rahoto wurin 'yan sanda ba, bayan wani abokin karatun jami'arta ya auka mata.

A cewar Megumi, su biyu suna zaune suna kallon talbijin ne a tare lokacin da ya fara tattaɓa ta Megumi da iskanci, wadda ta ce "A'a".