You are here: HomeAfricaBBC2021 03 29Article 1217917

BBC Hausa of Monday, 29 March 2021

Source: bbc.com

Akalla mutum 32 sun hallaka a hatsarin jirgin kasa a Masar

Akalla mutum 32 sun hallaka yayin da 165 suka jikkata a hatsarin jirgin kasa a tsakiyar kasar Masar, a cewar jami'ai.

Taraguna sun kauce kuma sun kife yayin da jiragen kasa biyu da ke dauke da fasinjoji suka yi karo da juna kusa da garin Tahta da ke Lardin Sohag.

Wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun taka birkin gaggawa na jirgin da ke gaba abin da ya sa jirgin da yake baya ya yi karo da shi, in ji hukumar kula sufurin jirgin kasa ta kasar.

Shugaba Abdul Fattah al Sisi ya sha alwashin hukunta wadanda suke da alhaki a kan al'amarin.

"Duk wanda ya haddasa wannan mummunan hatsarin ta hanyar sakaci ko rashawa, ko wani abu makamancin haka, dole ne a hukunta shi ba tare da bata locai ba." Ya ce a shafinsa na twitter.

Al'amarin ya faru ne a wani wuri mai nisan kilomita 365 da birnin Alkahira.

Daya daga cikin jiragen kasa na tafiya ne tsakanin garin Luxor da ke kudanci da tashar ruwa ta Iskandriya yayin da dayan na tafiya ne tsakanin birnin Alkahira a garin Aswan da ke kudanci.

An tura da motocin daukar marasa lafiya sama da saba'in zuwa wurin da al'amarin ya faru domin su wuce da wadanda suka samu raunuka zuwa asibiti.

Join our Newsletter