You are here: HomeAfricaBBC2023 05 25Article 1773908

BBC Hausa of Thursday, 25 May 2023

Source: BBC

Abu biyar kan mutumin da ke ƙalubalantar Trump a jam`iyyar Republican

Ron DeSantis Ron DeSantis

Ron DeSantis ya bayyana ƙudirinsa na tsayawa takarar shugaban Amurka a ƙarƙashin jam`iyyar Republican a zaɓen 2024.

Ana hasashen cewa gwamnan na Florida zai zama babban abokin hamayyar Donald Trump a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

A halin yanzu Donald Trump ne ake kallo a matsayin na gaba-gaba a neman takarar ƙarƙashin jam'iyyar Republican.

Wane ne DeSantis?

An haife Ron DeSantis a Jacksonville da ke jihar Florida ta ƙasar Amurka, a shekara ta 1978.

Mista DeSantis ɗan siyasa ne a Amurka kuma tsohon jami'in soji wanda shi ne gwamnan jihar Florida na 46, wanda a ka zaɓa 2018.

DeSantis ya yi karatu a jami`ar YALE da kuma Havard Law School.

A cikin shekara ta biyu na karatunsa a Harvard ne ya fara aiki a rundunar sojin ruwa ta Amurka, inda ya yi aiki a ɓangaren shari'a.

Ayyukansa na a lokacin sun hada da yin aiki tare da wadanda ake tsare da su a Guantanamo Bay, da kuma aiki a matsayin mai bayar da shawara kan harkokin shari'a ga fitattun sojojin ruwan Amurka da aka tura zuwa yaƙi a Iraki.

An sallame shi daga aikin soja a 2010, kuma a daidai wannan lokacin ne ya hadu da matarsa, Casey, wadda ƴar jarida ce a wani gidan talabijin.

Ita ce ta taimaka wajen tattara kudade domin taimaka wa waɗanda guguwar Ian ta ɗaiɗaita a 2022.

An fara zaben DeSantis a majalisar dokoki ne cikin shekara ta 2012, kuma an sake zaɓen sa a shekara 2014 da 2016.

Bayan kwashe shekara biyar a majalisar dokokin Amurka - Mista DeSantis ya bayyana aniyarsa ta takarar gwamnan jihar Florida, inda ya samu cikakken goyon bayan shugaba Donald Trump.

A farko-farkon siyasarsa a Florida, DeSantis ya rinƙa hanƙoron ganin an rage kashe kuɗin gwamnati da rage haraji da kuma nuna adawarsa ƙarara da gwamnatin Obama.

An rantsar da shi a matsayin gwamnan Florida a watan Janairu, 2019.

Ba kamar sauran gwamnonin wasu jihohin ba, a matsayinsa na gwama, DeSantis yi ƙi ɗaukar mataka masu tsauri na yaƙi da yaɗuwar cutar korona.

Ya kuma ƙarfafa ƴancin mallakar bindiga da na aiwatar da hukuncin kisa, ya tsaurara dkokin shige da fice ba bisa ka'ida ba, sannan ya sanya hannu kan wani kudirin doka da ya haramta zubar da ciki bayan makonni shida.

Ɗaukakar daraja da Mista DeSantis ke samu na fuskantar suka daga tsohon uban-gidansa a siyasance Donald Trump, wanda ya sha iƙirarin cewa shi ne silar nasarar da gwamnan ya samu a zaben 2018.