You are here: HomeNews2023 04 13Article 1748852

BBC Hausa of Thursday, 13 April 2023

Source: BBC

Yaƙin Ukraine: Sojojin Rasha na ja-in-ja kan adadin mace-macen yaƙi

Sojojin Rasha Sojojin Rasha

Takardun sirrin Amurka da aka kwarmata sun bankaɗa yadda ɓangarorin dakarun tsaron Rasha suka samu rashin jituwa lamarin da ya sa har aka zargi ma'aikatar tsaro da rage yawan mutanen da suka mutu lokacin yaƙi a Yukren.

Rasha dai na ba ta cika yawan magana a bainar jama'a game da yawan mace-macen dakarunta a fagen yaƙi.

Sai dai takardun sirrin sun nuna jami'an tsaron leƙen asirin Rasha FSB na iƙirarin cewa hukumomi ba sa haɗa ƙirge da mace-macen Dakarun Tsaron Ƙasa na Rasha da sojojin haya na Wagner da kuma wasu.

Rasha dai tuni ta yi gargaɗin cewa bayanan da aka kwarmata ɗin mai yiwuwa na jabu ne, kuma da gangan Amurka ta yasar da su.

Sai dai, bayanan sun tabbatar da abubuwan da tun tuni aka sani: cewa sojojin Rasha da hukumomin tsaro sun yi ta samun saɓani game da yadda ake tafiyar da yaƙin na Yukren, kuma Rasha ta yi ta gujewa faɗar adadin dakarunta da suka mutu ko suka jikkata a bainar jama'a.

Lissafin hukumar leƙen asiri ta FSB da aka ba da bayani mutuwar kusan 110,000 a watan Fabrairu ya yi matuƙar gaza adadin wannan mako da aka samu kwanan baya a takardun Amurka da aka kwarmata, wanda ya ƙiyasta cewa Rasha ta yi asarar mutane tsakanin 189,500 zuwa 223,000, yayin da mutum 35,500-43,000 suka mutu a fagen daga.

Alƙaluman Rasha na baya-bayan nan a hukumance an fitar da su ne a watan Satumban bara, lokacin da ta tabbatar da mutuwar soja 5,937.

Irin waɗannan takardu da aka kwarmata sun ce rage yawan mutanen da aka kashe ko aka jikkata a tsarin tafi da harkoki na nuna "ci gaba da ƙiyawar" sojoji wajen kai labarai marasa daɗi ga manyan jagororin soji.

Sau da yawa, masharhanta kan nuna cewa ana kange Shugaba Vladimir Putin daga sanin haƙiƙanin asarar da Rasha ke tafkawa a fagen daga, kuma wannan ƙiyasi ga alama ana samo su ne ta hanyar kutse cikin layukan sadarwa.

Wata takardar bayanan asirin wadda aka yi wa tambari da babban sirri ta yi bayani a kan wasu "bayanan yaƙi" tsakanin ma'aikatar tsaro da kuma shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner Yevgeny Prigozhin a watan Fabrairu.

Prigozhin ya sha zargin sojoji da dakatar da safarar makamai, yayin da dakarunsa ke fafatawa da nufin ƙwace Bakhmut a gabashin Yukren.

Bayanan kwarmaton sun kuma ambato jami'an ma'aikatar suna nuna cewa suna neman "abokan ƙawancen da za su faɗa da dakarun Prigozhin maimakon su hakan da kansu".

Babban abin bankaɗar dai, shi ne bin diddigin da aka yi na takardun sirrin ya tabbatar da cewa gagarumar asarar da Dakarun Tsaro na Ƙasa ko Rosgvardia suka yi "mai yiwuwa zai daƙile ƙoƙarin hukumomin Moscow wajen tsare dukkan yankunan da ta mamaye kuma ta haɗe da ƙasarta".

Dakarun rundunar Rosgvardia sun shiga cikin yaƙin kuma sun taimaka wajen shirya ƙuri'un raba gardama da Rasha ta yi maguɗi wadanda suka sa Putin ya haɗe yankunan Yukren huɗu da ƙasarsa a cikin watan Satumban da ya wuce.

Abin da aka sani game da mutumin da ya kwarmata bayanan asirin ƙalilan ne, sai dai jaridar Washinton Post ta ruwaito cewa wani ɗan bindiga ɗaɗi ne lokacin da yake cikin shekarunsa na ashirin sa'ar da yake aiki a wani sansanin sojojin Amurka.

A cewar Washington Post, mai kwarmaton bayanan sirrin ya saurari bayanan sannan ya rubuta su kafin daga bisani, ya buga abin da ya gani ƙunshe a takardun sirrin, daga nan kuma ya wallafa hotunan takardun.

Daga cikin hotunan takardun da aka wallafa hotunan, akwai ɗaya da ke nuna ƙididdigar da Amurka ta yi wa "yaƙin mai ƙare ƙarfi" na Rasha a lardin Donbas da ke gabashin Yukren. Inda ta ce matuƙar ba wata "farfaɗowar da ba a yi tsammani ba" dakarun Rasha suka yi, ukren za ta iya kassara manufofin Rasha na shiga wannan yaƙi "abin da zai zama sanadin wani yaƙi na tsawon lokaci har gaban shekara ta 2023".

Mataimakin ministan harkokin wajen Rasha Sergei Ryabkov ya nuna cewa mai yiwuwa da gangan Amurka ta fito da takardun bayanan.

A matsayinta na wani "ɓangare a yaƙin" ya ce gwamnatin Washington mai yiwuwa tana nema hanyar da za ta "rufta abokan gaba wato Tarayyar Rasha".