You are here: HomeNews2021 05 06Article 1253158

BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: www.bbc.com

Matsalar tsaro: Ƴan bindiga sun sace 'mutum 100' a jihar Neja

Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari tare da garkuwa da mutane kusan 100 a garin Shadaɗi Ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari tare da garkuwa da mutane kusan 100 a garin Shadaɗi

Rahotanni daga jihar Neja da ke tsakiyar Najeriya na cewa ƴan bindiga sun kai ƙazamin hari tare da garkuwa da mutane kusan 100 a garin Shadaɗi, in ji mazauna garin.

Harin da aka kai jiya na zuwa ne a dai-dai lokacin da matsalolin tsaro ke sake rincaɓewa a yankunan Neja tun bayan da gwamnan jihar ya tabbatar da cewa ƴan Boko Haram sun shiga garin.

Yanzu haka jama'ar garin Shadaɗi da ke karamar hukumar Mariga na cewa dubbai sun tsere bayan da ƴan bindiga sun kai masu hari.

Sannan akwai masu cewa waɗanda aka kashe sun haura mutum 100, adadin da gwamnatin jihar ta ce bai kai haka ba.

Abin da ƴan garin ke cewa

Wani mazaunan garin da BBC ta tattauna da shi ya ce ƴan bindiga sama da dubu ne suka dirar musu tare da kashe mutum 8 da jikkata 4.

A cewar mutum da ya bukaci a sakaya sunansa kusan duk ƴan garin sun tsere zuwa garuruwa maƙwabta irinsu kwantagora.

Kwamishinan yaɗa labaran jihar Nejar, Alhaji Sani Idris, ya tabbatar da kai harin sai dai ya ce adadin mutanen da ake cewa an sace bai kai 100 ba.

Ya ce yanzu haka suna kan kididdiga domin tabbatar da adadin mutanen da harin ya ritsa da su kuma tuni sun nemi haɗin-gwiwar gwamnatin tarayya.

Sai dai babu ƙarin haske kan ko wadanda suka kai harin ƴan Boko Haram ne.

Jihar Kaduna ma ta tsinci kanta cikin irin wannan yanayi, inda wasu ƴan bindigan suka kai hari a wasu majami'u, har suka kashe mutane biyu, aka kuma sace wasu.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce, an sami nasarar kubutar da mutanen da aka sace.

Karin haske

Matsalolin tsaro dai a Najeriya a kullum na sake rincaɓewa batun da ke sake jefa tsoro da zaman dar-dar tsakanin ƴan ƙasar musamman mazauna kauyuka.

Masana na ganin akwai gazawar shugabanci kan yadda tsaro ke ƙara taɓarɓarewa.

Su na mai cewa halin da ƙasar take ciki a yanzu abu ne mai matukar tayar da hankali saboda girman matsalar tsaro da ke ci gaba da ɗaukar sabbin salo.

Sannan a koda yaushe suna jadada bukatar ƙara yawan jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji sannan a saki kayan aiki tare da sa ido ga yadda za a kashe kudaden.

Gwamnatin dai na cewa tana iya bakin ƙokarinta domin shawo kan matsalolin tsaron ƙasar.

Join our Newsletter