You are here: HomeAfricaBBC2023 06 12Article 1784306

BBC Hausa of Monday, 12 June 2023

Source: BBC

Real Madrid ta yi wa Brahim Diaz kiranye daga AC Milan

Brahim Diaz Brahim Diaz

Brahim Diaz ya sake komawa ƙungiyarsa Real Madrid a bana, bayan kaka uku yana wasannin aro a AC Milan.

Mai shekara 23, ya lashe kofin Serie A tare da Milan a 2021/21 sannan ya buga wasan daf da ƙarshe a Champions League a bana, inda Inter Milan ta fitar da su.

Real Madrid ta dauki Brahim a Janairun 2019 daga Manchester City, wanda ya dauki kofin La Liga a Santiago Bernabeu a kakar 2019/20 da Spanish Super Cup a 2020.

An bayar da shi aro ga AC Milan a cikin Satumbar 2020, inda ya yi kaka uku tare da cin ƙwallo 18 a dukkan fafatawar da ya yi wa Milan.

Ya fara taka leda a matashin dan wasa a Malaga, daga nan ya koma Manchester City, ya fara taka leda a Ingila a karawa da Swansea a EFL Cup a 2016/17 yana da shekara 17.

A kakar 2017/18 ya fara buga Premier League da FA Cup, wanda ya bayar da gudunmuwar da City ta lashe lik da League Cup.

Haka kuma ya ɗauki Community Shield a dai Manchester City.

Ƙungiyoyin da ya buga a matakin ƙwararren ɗan wasa:

  • Manchester City youth teams (2013-2018)


  • Manchester City (2018-2019)


  • Real Madrid (2019-2020)


  • Milan (2020-2023)
  • Real Madrid (2023- )


  • Kofunan da ya lashe kawo yanzu:

    Kofin LaLiga 1

    Kofin Spanish Super Cup 1

    Kofin Serie A 1

    Kofin Premier League 1

    Kofin League Cup 2

    Kofin Community Shield 1