You are here: HomeAfricaBBC2024 01 06Article 1908545

BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Mario Zagallo ya mutu yana da shekara 92

Fitatcen dan kwallon Brazil, Mario Zagalo wanda ya lashe kofin duniya huɗu a matakin ɗan wasa da koci ya mutu yana da shekara 92.

Zagallo, wanda ke buga wasa daga gefen gaba, yana cikin tawagar Brazil da ta lashe kofin duniya biyu a jere, wato a 1958 da kuma 1962.

Ya horar da tawagar da ake cewa ba kamarta a fagen taka leda a duniya har kawo yanzu da ta hada da Pele da Jairzinho da Carlos Alberto da suka dauki kofi a1970.

Kofin duniya na karshe da Zagalo ya dauka shi ne a matakin mataimakin koci, Carlos Alberto Parreira a 1994.

Ya karbi ragamar horar da Brazil zuwa karawar ƙarshe a gasar kofin duniya a 1998, inda Faransa mai masaukin baki ta yi nasara.

Zagallo shi ne na farko da ya lashe kofin duniya a matakin ɗan wasa da koci - daga baya Franz Beckenbauer na Jamus da Didier Deschamps na Faransa suka bi baya.

Brazil ce kan gaba a yawan lashe kofin duniya mai biyar a tarihi, inda Zagalo ya bayar da gudunmuwar da ta dauki hudu daga ciki.