You are here: HomeAfricaBBC2023 07 25Article 1811930

BBC Hausa of Tuesday, 25 July 2023

Source: BBC

Ƙungiyoyi na rububin Mbappe, Man Utd na nazari kan Muani

Kylian Mbappe Kylian Mbappe

Chelsea da Manchester United da Tottenham za su kasance cikin kungiyoyin da suke gogayyar zawarcin Kylian Mbappe, bayan da Paris St-Germain ta samu tayin Fam miliyan 259 wanda ba a taba sayen wani dan wasa ba, daga Al-Hilal ta Saudiyya a kan dan wasan. (Telegraph)

Kuma kungiyar ta Al Hilal ta shirya bai wa Mbappe albashin da ya kai Yuro miliyan 200 (£172m) a shekara. (Fabrizio Romano).

Idan har Mbappe ya je Al-Hilal din to kuwa zai kasance ne a can tsawon shekara daya kawai, saboda PSG ta san cewa shugaban Real Madrid Florentino Perez da dan wasan sun yi yarjejeniya ta ya koma can a shekara mai zuwa. (Times)

Ita kuwa Barcelona ta nesanta kanta daga maganar Mbappen duk da rahotannin da ke cewa ta tattauna da PSG. (Marca)

Idan har Mbappe ya tafi Saudiyya to PSG za ta biya Fam miliyan 100 da Tottenham ta sanya a kan Harry Kane ta saye shi, ko da yake har yanzu Bayern Munich na da kwarin gwiwa wajensu kyaftin din na Ingila zai je. (Independent)

Manchester United na shirin gabatar da tayin sayen matashin dan wasan Atalanta Rasmus Hojlund, dan Denmark, wannan makon. (Mail)

United na son biyan Fam miliyan 60 ne kawai a kan dan wasan mai shekara 20, wanda hakan ya kasa abin da kungiyar ta Italiya ke nema a kanshi Fam miliyan 86.5. (Times)

Haka kuma kungiyar ta Old Trafford na nazari a kan dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani, dan Faransa, kuma kociyanta Erik ten Hag na sha'awar dan gaban Ajax Mohammed Kudus, na Ghana mai shekara 22, wanda ake alakantawa da tafiya Chelsea. (Mirror)

Harwayau Ten Hag na son ya kara karfin masu tsaron ragar kungiyar, inda yake son sayen golan Fenerbahce Altay Bayindir mai kama wa tawagar kasar Turkiyya. (Goal)

A wani labarin kuma kungiyar Saudiyyar, ta Al Hilal tana dab da cimma yarjejeniya da Fulham kan sayen dan wasan Serbia Aleksandar Mitrovic, mai kai hari. (90min)

Dan wasan tsakiya na Ingila Jordan Henderson, mai shekara 33, ya yi sallama da ma'aikata da 'yan wasan Liverpool yayin da yake shirin tafiya Al-Ettifaq ta Saudiyya. (Mail)

Everton na dab da sayen dan wasan Almeria mai kai hari, El Bilal Toure, duk da cewa Atalanta na kokarin sayen matashin mai shekara 21, na tawagar Mali. (Football Insider)

Tottenham da West Ham ne a kan gaba a masu zawarcin dan wasan tsakiya na Ingila Conor Gallagher, wanda zai bar Chelsea, saboda kungiyar tana ganin ba ta bukatarsa. (Standard)

Kokarin Chelsea na sayen dan wasan tsakiya na Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21, daga Brighton ya gamu da cikas, saboda bukatar kungiyarsa ta neman a hada mata da matashin dan baya Levi Colwill mai shekara 20 a cinikin. (Guardian)

Spurs da Nottingham Forest sun tuntubi Juventus a kan ta sayar musu da dan bayanta Andrea Cambiaso, dan Italiya. (Tuttosport)

Inter Milan ta yi tayin bai wa Aston Villa Yuro miliyan 15 (£12.95m) a kan golanta Emiliano Martinez, dan Argentina bayan da Andre Onana ya tafi Manchester United. (TyC Sports Argentina)

Dan wasan tsakiya na Leicester City Hamza Choudhury, yana son a kammala magana kan ba shi dogon kwantiragi a kungiyar nan da lokacin fara kakar bana, domin Southampton na nuna sha'awarta a kanshi. (Mail)