You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809578

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

‘Abin da ya fi ci min rai bayan na kamu da HIV shi ne rashin aure’

Hoton alama Hoton alama

Talatu (wanda ba sunanta ba kenan) mazauniyar garin Kano ce da ke arewa maso yammacin Najeriya, tana rayuwa da cutar nan mai karya garkuwar jikin ɗan adam wadda ake kira da HIV.

Cutar HIV na buƙatar kulawa wanda kuma gaza samun kulawar kan kai ta mataki na gaba na AIDS.

‘Yar shekara 35 ɗin ta bayyana wasu abubuwa uku da tace suna ci mata tuwo kwarya, ciki har da rashin samun haihuwa.

Matar wadda ta kwashe shekara 19 ɗauke da cutar ta ce daga ita sai mahaifiyarta da wasu mutane ƙalilan ne suka san tana ɗauke da cutar, saboda gudun tsangwama.