You are here: HomeAfricaBBC2023 08 12Article 1823297

BBC Hausa of Saturday, 12 August 2023

Source: BBC

West Ham ta kammala ɗaukar Alvarez daga Ajax

Edson Alvarez Edson Alvarez

West Ham ta kammala ɗaukar Edson Alvarez daga Ajax kan fam miliyan 35.

Mai shekara 25, yana cikin 'yan kwallon tawagar Mexico da suka lashe Concacaf Gold Cup a Amurka a kakar nan.

Alvarez shi ne na farko da West Ham ta ɗauka, tun bayan da ta sayar da Declan Rice ga Arsenal kan fam miliyan 105.

West Ham ta kulla yarjejeniya da Manchester United don sayen Harry Maguire da James Ward-Prowse na Southampton kan fam miliyan 60.

Haka kuma West Ham na fatan sayen Cole Palmer daga Manchester City.