You are here: HomeAfricaBBC2023 06 08Article 1782212

BBC Hausa of Thursday, 8 June 2023

Source: BBC

N'Golo Kante ya koma Al-Ittihad ta Saudi Arabia

N'Golo Kante N'Golo Kante

N'Golo Kante ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku da Al-Ittihad ta Saudiyya, kamar yadda wata majiya ta sanar wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Dan kwallon tawagar Faransa ya je kungiyar kwana daya bayan tsohon dan wasan Real Madrid, Karim Benzema ya koma Al-Ittihad.

Kante, mai shekara 32, ya je an auna koshin lafiyarsa daga baya ya saka hannu kan kunshin yarjejeniya, kamar yadda majiyar ta sanar da labarin cewar ba a ba ta izinin bayyana batun daukar Kante ba.

Kante wanda ya bar Chelsea a kakar nan, ya lashe kofin duniya a 2018 a Rasha tare da tawagar Faransa, kuma a halin yanzu yana fama da raunin da ya yi jinyar wata shida.

Majiyar ba ta fayyace kan kudin da Kante ya amince da kunshin yarjejeniyar buga gasar kwallon Saudi Arabia ba.

Ranar Talata Al-Ittihad ta sanar da daukar Benzema, mai shekara 35, shima kan kwantiragin kaka uku, bayan da yarjejeniyar ta kare a bana da Real Madrid.

Benzema da Kante da kyaftin din Argentina, Lionel Messi, na cikin 'yan kwallo 10 da Saudiyya ta tsara dauka, domin bugawa a gasar tamaula na kasar.