You are here: HomeAfricaBBC2023 06 06Article 1781330

BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

Yaro Bafalasɗine ya mutu bayan harbin da sojojin Isra'ila suka yi

Hoton alama Hoton alama

Wani yaro Bafalasɗine mai shekara uku ya rasu kwana huɗu bayan harbin da sojojin Isra'ila suka yi masa a kai.

Dakarun Isra'ila sun harbe Mohammed Tamimi ne tare da mahaifinsa a lokacin da suke barin gidansu a Nabi Saleh cikin yankin Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Sojojin Isra'ilar sun ce dakarunsu sun buɗe wuta ne a ƙoƙarin da suke yi na farautar wasu 'yan bindiga biyu da suka buɗe wuta a kusa da gine-ginen Yahudawa.

A wata sanarwa da suka fitar, sun ce sun yi nadamar buɗe wuta a kan fararen hular.

Wani ɗan fafutukar Falasɗin kuma ɗan jarida Bilal Tamimi - wanda shi ma ya samu raunuka sanadin harbi, ya ce dakarun sojin Isra'ila sun tsaya a bakin unguwar, suna jiran isar wata ƙaramar mota domin yi mata kwanton ɓauna, daga nan kuma sai suka buɗe wuta a lokacin da ta tunkari ƙofar unguwar.

Rahotonni sun ce jirgin sojin Isra'ila mai sauƙar ungulu ne ya ɗauki yaron inda ya garzaya da shi asibitin yara da ke Safra domin yi masa magani a raunukan da ya ji a kansa, to amma bayan kwana huɗu sai yaron ya cika.

Sojojin na Isra'ila sun wallafa wani bidiyo da ke nuna wasu mutane biyu na harbi a unguwar Yahudawa ta Halamish.

Sun ce martanin da sojojinsu suka mayar ne ya yi sanadin ritsawa da Falasɗinawa biyu ciki har da ƙaramin yaron.

''Mun yi nadamar raunata fararen hula a wannan martani, kuma muna nazari a kan harin, sannan mun yi bakin iyakar ƙoƙarinmu domin kiyaye sake aukuwar haka a nan gaba'', kamar yadda sanarwar sojojin Isra'ilar ta bayyana.

Gine-ginen Halamish, waɗanda aka yi cikin 1970, sun kasance wata cibiyar rikici tsakanin unguwar da ƙauyukan Palasɗinawa masu maƙwabtaka.

An kwashe shekaru ana gudanar da zanga-zanga duk ranar Juma'a a unguwar Nabi Saleh, inda mazauna unguwar ke nuna adawa a kan ƙwace musu filaye tare da ƙoramun unguwar.

Hakan kuma a lokuta da dama yakan haifar da hatsaniya tsakaninsu da sojojin Isra'ila waɗanda ke amfani da hayaƙi mai sa hawaye da harsasan roba domin tarwatsa su.

Falasɗinawa 150 ne sojojin Isra'ila da mazauna Gaɓar Yamma da Kogin Jordan, da Gabashin Kudus da Zirin Gaza, suka kashe tun farkon wannan shekarar.

Wannan adadi ya haɗar da 'yan bindiga da fareren hula.

Haka kuma mutum 23 ne aka kashe a ɓangaren Isara'ila ciki har da 'yan ƙasashen waje biyu da wani ma'aikacin Falasɗinu da kuma wani jami'in tsaron Isar'ila, a rikice-rikice masu alaƙa tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.

A duka ɓangarorin biyu akwai yara cikin waɗanda aka kashen.

Mohammed Tamimi shi ne mafi ƙarancin shekaru cikin Falasɗinawan da aka kashe a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

A yanzu haka akwai Yahudawa kusan 700,000 da ke zaune a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Gabashin Kudus.

Dokokin ƙasashen duniya dai na kallon zaman da suke yi a matsayin wanda ba ya kan ƙa'ida.

Sai dai isra'ila ta ƙi amincewa da hakan.