You are here: HomeAfricaBBC2023 06 06Article 1781306

BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

Wata shida bayan kisan makiyaya a Nasarawa har yanzu ba a yi bincike ba - HRW

Jirgin sama na yaki Jirgin sama na yaki

Kisan fararen hula 39 sakamakon harin sama da sojoji suka kai ranar 24 ga watan Janairun 2023 a garin Kwatiri da ke jihar Nasarawa wani mummunan lamari ne da ke buƙatar a yi adalci.

To sai dai har yanzu hukumomin Najeriya ba su bayar da cikakken bayani kan harin ba - in ji ƙungiyar kare haƙƙin dan adam ta Human Rights watch.

Human Rights watch dai ta yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da an gudanar da bincike mai zaman kansa cikin gaggawa, ba tare da nuna son kai ba.

Kwatiri dai wani ƙaramin matsuguni a jihar Nasarawa da ke Arewacin Najeriya.

Kusan watanni shida da faruwar lamarin, rundunar sojin saman Najeriya ta amince a karon farko, a matsayin martani ga wani bincike da kungiyar kare haƙƙin bil-Adama ta Human Rights Watch ta yi, game da kai harin ta sama.

Ta ce, wani sashe ne na rundunar sojin sama na Operation Whirl Stroke, rundunar hadin gwiwa ta sojoji, ‘yan sanda, da jami’an tsaro na jihar da aka tura domin magance matsalolin tsaro a jihar Nasarawa da kewaye.

Rundunar sojin saman ta ce ta kai harin ne a matsayin mayar da martani ga ayyukan "da ake zargin na ta'addanci ne" amma ba ta bayar da cikakken bayani ba.

Anietie Ewang, mai bincike a Afirka a Human Rights Watch ta ce "jinkirin da sojoji suka yi na amincewa da kisan mutane har 39 da kuma raunata fararen hula kawai ya kara munana tunanin mutane ne kan lamarin.

"Ya kamata sojojin Najeriya su bayar da cikakken bayani kan abin da suka yi, su kuma biya diyya ta kudi tare da tallafa wa iyalan waɗanda abin ya shafa."

Tun daga shekarar 2017, sama da mutane 300 ne aka bayar da rahoton cewa an kashe su ta hanyar kai hare-hare ta sama da rundunar sojin saman Najeriya ta yi ikirarin cewa an yi niyyar kai wa ne kan ‘yan bindiga ko kuma ‘yan kungiyar Boko Haram amma a maimakon haka sai ya faɗa wa fararen hula.

A ranar 25 ga watan Janairu ne gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya shaida wa kafafen yada labarai na Najeriya cewa, harin da aka kai ta sama ya afka wa wasu gungun makiyaya ne a wani yanki na karamar hukumar Doma da ke jihar, wani jirgin ne da ba a tantance ba ya kai harin.

A tsakanin ranakun 13 zuwa 15 ga Maris, Human Rights Watch ta yi hira da mutane 12, ciki har da mutane biyu da suka tsira daga harin ta sama da kuma wasu 'yan uwan mutane bakwai da aka kashe.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta kuma yi nazari tare da tantance wasu hotuna guda takwas da ke nuna wasu gawarwakin, sannan a ranar 14 ga watan Maris ta ziyarci wani kabari da aka binne gawarwaki 31.

A ranar 3 ga watan Mayu ne kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta rubuta wa babban hafsan hafsoshin sojin sama na Najeriya, wanda ke kula da rundunar sojin sama da ke gudanar da ayyukan soji, da kuma babban hafsan tsaron da ke kula da dukkan rundunonin soji ciki har da na sojojin sama, domin su bayar da cikakkun bayanai.

A martanin da ya mayar a ranar 17 ga watan Mayu, Air Commodore D. D. Pwajok, a madadin hafsan hafsoshin sojin sama, ya amince da cewa rundunar ta gudanar da harin ne bayan samun “sahihan bayanan sirri da kuma hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro da hukumomin jihar Nasarawa suka yi.”

Wasikar ta bayanin da ɗauko ta sama daga rundunar sojin sama ya nuna motsin “’yan ta’adda da ake zargi, wanda aka yanke shawarar cewa za a kai harin., amma dai bayanin bai amsa wasu tambayoyi masu mahimmanci ba, ciki har da yadda aka yi la'akari da bayanan da ake zargi da barazanar da kuma tabbatar da su.

"Ya kamata mahukuntan Najeriya su bayyana kudurinsu na kare hakkin 'yan kasa ta hanyar gudanar da bincike cikin gaggawa, da bayyana sakamakon binciken, da kuma daukar matakai na tabbatar da adalci da rikon amana," in ji Ewang.

"Ya kamata gwamnatocin kasashen waje su goyi bayan wannan yunƙurin sannan su kuma matsa wa hukumomi su ɗauki matakin bincikar ayyukansu na tsaro tare da ɗaukar matakan da suka dace don guje wa cutar da fararen hula."

Hare-haren sama na kuskure daga sojojin Najeriya

A cikin watan Fabrairu, SBM Intelligence, wata ƙungiyar bincike a Najeriya da ke mayar da hankali kan rikice-rikice, ta gano karuwar hare-haren kuskuren da sojojin saman Najeriya ke yi tun a shekarar 2017, lokacin da wani harin da sojojin saman Najeriya suka kai kan sansanin 'yan gudun hijira da ke Rann na jihar Borno, inda aka kashe mutane 70 da kuma jikkata sama da 120.

Hukumomin kasar sun dauki alhakin kai harin ta sama, wanda suka ce kuskure ne, amma har yanzu ba su yi bincike tare da biyan diyya ga wadanda lamarin ya rutsa da su ba.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar Nasarawa ya shaida wa kungiyar Human Rights Watch cewa, kafin faruwar lamarin Kwatiri, an samu wasu hare-haren bam da ba a bayyana ba a jihar Nasarawa, ciki har da wanda aka kai a watan Nuwambar 2022 a yankin Adudu na karamar hukumar Obi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 10 ciki har da wata uwa mai shayarwa da ɗanta.

A watan Oktoban 2022, rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa ta bude wani bincike kan harin da aka kai ta sama kan fararen hula bisa kuskure amma ba ta bayar da wani karin bayani ba.