BBC Hausa of Tuesday, 6 June 2023

Source: BBC

Al-Ittihad ta kammala ɗaukar Karim Benzema

Karim Benzema Karim Benzema

Mai riƙe da Ballon d'Or, Karim Benzema ya koma Al-Ittihad ta Saudi Arabia kan yarjejeniyar kaka uku, bayan da ya bar Real Madrid a bana.

Tsohon ɗan ƙwallon Faransa, mai shekara 35 ya lashe kofi 25 a Santiago Bernabeu - ciki har da Champions League biyar da La Liga huɗu a kaka 14 da ya yi a Real Madrid.

Ya ci ƙwallo 354 a ƙungiyar ta Sifaniya, wanda shi ne na biyu a yawan ci wa ƙungiyar ƙwallaye a tarihi, bayan Cristiano Ronaldo.

Ronaldo, wanda ya ci wa Real Madrid kwallo 450, yana taka leda a Al Nassr ta Saudi Arabia.

Tsohon kociyan Wolverhampton da kuma Totteham, Nuno Espirito Santos ne kociyan Al-Ittihad a yanzu haka.

Benzema ya yi wa Real wasa 648, bayan da ya koma ƙungiyar a 2009 daga Lyon.

Ana kuma alaƙanta Lionel Messi da cewar zai koma taka leda a Saudi Arabia, bayan da ya gama yi wa Paris St Germain tamaula ranar Asabar.

Messi, kyaftin din Argentina tsohon ɗan wasan Barcelona ya yi kaka biyu a PSG da lashe Ligue 1 biyu.