You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780604

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Benzema zai koma Al-Ittihad, Madrid za ta dauki Kane

Karim Benzema Karim Benzema

Manchester City ta na ganin tayin da ta yi zai iya lallabar dan wasan Norway Erling Haaland mai shekara 22 ya ci gaba da zama a kungiyar tare da daina hangen Real Madrid. (Telegraph - subscription required)

Tuni Real Madrid ta tuntubi Tottenham da kuma Harry Kane kan yiwuwar daukar dan wasan Ingilan mai shekara 29 domin ya maye gurbin Karim Benzema mai shekara 35 wanda ya tabbatar da cewa zai bar Madrid din a karshen kakar nan. (Marca - in Spanish)

Har'ilayau Real Madrid din tana kan hanyar daukar dan wasan Jamus Kai Havertz mai shekara 23 daga Chelsea. (Bild - in German)

Manchester United za ta bayar da fam miliyan 50 kan dan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount mai skeara 24 daga Chelsea sannan za ta lallaba Tottenham ta sayar da Kane (Telegraph - subscription required)

Ana sa ran Benzema zai koma Al-Ittihad ta Saudiyya a wani kwantiragin shekara biyu. (Al-Ekhbariya, via L'Equipe)

Alfanun da Inter Miami ta ce dan wasan gaba na Argentina da kuma Paris St-Germain Lionel Messi mai shekara 35 zai samu idan ya koma gareta sun hada da talla ga kamfanonin Apple da kuma Adidas amma duk da haka alfanun bai kai wanda zai samu idan ya tafi Saudiyya ba. (Guillem Balague)

Paris St-Germain na zawarcin tsohon shugaban Bayern Munich Julian Nagelsmann domin ya maye gurbin Christophe Galtier a matsayin Kociye tare da daukar Thierry Henry a matsayin mataimakinsa. (Foot Mercato - in French)

A na sa ran Chelsea za ta kammala sanya hannu don dauko Manuel Ugarte dan shekara 22 daga Sporting Lisbon tare da biyansa fam miliyan 52. (Record - in Portuguese)

Chelsea ta nunawa Paris St-Germain sauri wajen daukar Ugarte bayan gwaggwaban tayi. (Mirror)