You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780592

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Farashin man fetur ya tashi a duniya bayan rage adadin da Saudiyya ke fitarwa

Hoton alama Hoton alama

Farashin ɗanyen man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan ƙasar Saudiyya ta ce za ta rage ganga miliyan ɗaya cikin abin da take fitarwa kullum a watan Yuli.

Sauran ƙasashe wakilan ƙungiyar ta Opec+, wadda wani rukunin ƙasashe masu arziƙin man fetur ce, ta amince da rage yawan man da take haƙowa a wani yunƙuri na ɗaga farashin da yake ta faɗuwa.

Ƙungiyar Opec+ na samar da kimanin kashi 40% na adadin ɗanyen man fetur ɗin duniya kuma duk wata shawara da za ta ɗauka game da man, na iya yin gagarumin tasiri a kan farashinsa.

A kasuwannin Asiya ranar Litinin, ɗanyen man fetur nau'in brent ya tashi da kimanin kashi 2.4% kafin ya daidaita a kan kuɗi kimanin $77 a kan duk ganga ɗaya.

Ƙungiyar Opec+ ta ce yawan man fetur da ƙasashenta ke haƙowa zai sake raguwa da ƙarin ganga miliyan 1.400 daga 2024.

Ganawar ta tsawon sa'a bakwai a ranar Lahadi da ƙasashe masu arziƙin man fetur ɗin suka yi ta zo ne sanadin faɗuwar da farashin man fetur ke ci gaba da yi a duniya.

Farashin ɗanyen man fetur ya ɗaga sama lokacin da Rasha ta mamaye Ukraine bara, amma a yanzu ya koma kan matakin da yake kai tun ma kafin fara yaƙi.

A watan Oktoban bara, ƙungiyar Opec+ wadda ke nufin Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Man fetur da Ƙawayenta ta amince ta rage yawan man da take haƙowa da ganga miliyan 2, kimanin kashi 2% na abin da duniya ke buƙata.

A Afrilun wannan shekara ƙungiyar ta sake rage yawan man fetur ɗin, wanda ta tsara zai kai har ƙarshen wannan shekara. Sai dai Mataimakin Firaministan Rasha Alexander Novak ya ce tattaunawar ta ranar Lahadi ta janyo "tsawaita yarjejeniyar har zuwa ƙarshen shekara ta 2024".

A ranar Lahadi, Ministan Makamashin Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Salman ya ce ƙasarsa na iya ci gaba da rage ganga miliya 1 har bayan watan Yuli idan ana buƙata.