You are here: HomeAfricaBBC2023 06 05Article 1780583

BBC Hausa of Monday, 5 June 2023

Source: BBC

Liverpool ta kusan ɗaukar Mac Allister daga Brighton

Liverpool ta kusan kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyan Brighton, Alexis Mac Allister Liverpool ta kusan kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyan Brighton, Alexis Mac Allister

Liverpool ta kusan kammala ɗaukar ɗan wasan tsakiyan Brighton, Alexis Mac Allister.

Mahaifin dan wasan mai shekara 24 da ake kira Carlos, wanda shine wakilinsa ya je wata tattaunawa a karshen mako kan makomar wanda ya lashe kofin duniya a Qatar a 2022.

An fahimci cewar dan wasan tawagar Argentina yana da kunshin kwantiragin fam miliyan 45 zuwa 55 ga duk kungiyar dake son sayensa, yarjejeniyarsa ba ta kare ba.

Dan wasan na Brighton wanda take ji da shi ya saka hannun kan ci gaba da taka leda a kungiyar cikin watan Oktoban bara, ana sa ran Liverpool za ta biya sauran yarjejeniyar dan kwallon.

A watan jiya kocin Brighton, Roberto De Zerbi ya ce ya kwan da sanin za a kwashe musu 'yan wasa da yawa, wadanda zai so su buga wa kungiyar gasar zakarun Turai a badi.

Brighton ta kare a mataki na shida a teburin Premier League da maki 62 da tazarar maki biyar tsakaninta da Liverpool ta biyar, wadanda za su kara a Europa League a badi.

Jurgen Klopp na fatan kara karfin kungiyar a badi, bayan da James Milner da Naby Keita da kuma Alex Oxlade-Chamberlain za su bar kungiyar a karshen kakar nan.

Haka kuma Liverpool na fatan zawarcin Mason Mount, wanda ke kakar karshe a kunshin yarjejeniyarsa a Chelsea, amma Manchester United na kan gaba wajen son sayen dan wasan.

Ana kuma alakanta Liverpool da batun sayen dan wasan Bayern Munich, Ryan Gravenberch da na Nice, Khephren Thuram da na Borussia Monchengladbach, Manu Kone.

Liverpool na fatan kammala daukar 'yan wasan da take son amfani da su a badi da wuri, domin ta fara gwada su tun daga 8 ga watan Yuli.