You are here: HomeAfricaBBC2023 05 31Article 1777607

BBC Hausa of Wednesday, 31 May 2023

Source: BBC

Karon farko an cinye Mourinho a wasan karshe a Zakarun Turai

Jose Mourinho Jose Mourinho

Sevilla ta lashe Europa League na bana, bayan da ta doke Roma a bugun fenariti ranar Laraba a Budapest.

Sevilla ta lashe kofi na bakwai jimilla da cin 4 -1 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, bayan da suka tashi 1-1 har da karin lokaci.

Roma ce ta fara cin kwallo ta hannun Paulo Dybala, saura minti goma su je hutun rabin lokaci.

Sevilla ta farke kwallon bayan da suka koma zagaye na biyu, sakamakon da Gianluca Mancini ya ci gida.

An raba katin gargadi mai ruwan dorawa 13 a wasan, inda aka bai wa 'yan wasa Roma bakwai na Sevilla shida, ita ce karawar da aka raba katin gargadi da yawa a tarihin gasar zakarun Turai.

Karo na biyu da suka fuskaci juna a tsakaninsu a Europa League, inda Sevilla ta ci 2-0 ranar 6 ga watan Agustan 2020.

Sevilla ce kan gaba a daukar wannan kofin, wadda ba ta taba rashin nasara ba a dukkan wasan da ta aki karawar karshe a gasar.

Shi kuwa kociyan Roma, Jose Mourinho wanda yake da tarihin lashe kofin zakarun Turai a duk wasan karshe, wannan karon ya kasa daukar na bana, kuma a karon farko a tarihi.

Mourinho, mai shekara 60 yana da kofin zakarun Turai biyar da ya dauka da suka hada da Champions League biyu da Europa League biyu da kuma Europa Conference League da ya lashe a kungiyar ta Italiya.

Har yanzu dai Mourinho yana kan-kan da Giovanni Trapattoni a matakin kociyoyin da suke da tarihin daukar kofin zakarun Turai biyar.

Roma ta barar da damar buga Champions League a badi, bayan da ba ta lashe Europa na bana.

Domin kungiyar tana ta shida a teburin babbar gasar tamaula ta Serie A, wadda za a karkare wasannin bana ranar Lahadi.