You are here: HomeAfricaBBC2023 05 31Article 1777592

BBC Hausa of Wednesday, 31 May 2023

Source: BBC

Klopp na sa ran gaba za ta yi kyau duk da rashin kokarin Liverpool

Jurgen Klopp, kocin Liverpool Jurgen Klopp, kocin Liverpool

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce akwai abubuwa da dama da za su sa shi farin ciki duk da mummunan bakin cikin da ya biyo bayan rashin samun damar buga gasar Zakarun Turai.

Nasarar da Man United ta yi a kan Chelsea da ci 4 da 1 ranar Alhamis ta ba ta gurbin gasar Zakarun Turai, tare da Man City da Arsenal da kuma Newcastle a kaka mai zuwa.

Klopp, wanda ke da tabbacin cewa kungiyarsa za ta zo ta biyar a gasar Premier ta bana, ya gaya wa manema labarai ranar Juma'a cewa yana da tabbacin Man United da Newscastle za su samu makin da suke bukata a wannan makon bayan kungiyarsa ta yi 1-1 da Aston Villa.

Hakan na nufin cewa Liverpool ta kasa samun damar shiga gasar badi bayan jera shekara shida tana buga gasar.

Klopp ya bayyana cewa Liverpool za ta yi fama da matsalar rashin kudi sakamakon gazawar da ta yi ta shiga gasar.

Ya ce duk da yake ba su biya ma masu goyon bayan kungiyar bukata ba, yana sa ran cewa hadin kan da 'yan kungiyar ke da shi zai taimaka wurin kawo nasarorin da ake bukata a kakar wasa ta gaba.